Sai da 'yan daba suka fara harbe-harbe kafin su bankawa gidan Igboho wuta, 'Yan sanda

Sai da 'yan daba suka fara harbe-harbe kafin su bankawa gidan Igboho wuta, 'Yan sanda

- Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta sanar da yadda 'yan daba suka dinga harbi kafin bankawa gidan Igboho wuta

- 'Yan daban cike da motoci biyu sun tsinkayi gidan Sunday Igboho wurin karfe 3:20 na dare inda suka kone shi

- CSP Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da cewa an fara bincike kan lamarin kuma za a tabbatar da hukunta 'yan daban

A yayin martani ga bankawa gidan Sunday Igboho da aka yi a Ibadan, rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta ce ta samu rahoton yadda wasu bata gari suka cika motoci biyu taf sannan suka bankawa gidan wuta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, CSP Olugbenga Fadeyi ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar kuma jaridar Vanguard ta gani a ranar Talata.

Fadeyi ya kara da cewa an sanar da 'yan sanda cewa an ji karar harbe-harbe kafin daga bisani a bankawa gidan wuta a yankin Soka da ke Ibadan.

Ya ce 'yan sanda sun fara bincike a kan aukuwar lamarin.

Sai da 'yan daba suka fara harbe-harbe kafin su bankawa gidan Igboho wuta, 'Yan sanda
Sai da 'yan daba suka fara harbe-harbe kafin su bankawa gidan Igboho wuta, 'Yan sanda. Hoto daga @Thecableng
Source: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar

An gano cewa an kone gidan ne wurin karfe 3 na asubar Talata bayan an dauke wuta cikin daren.

Takardar da 'yan sandan suka fitar ta ce: "Wurin karfe 3:20 na asubar 26/01/2021 muka samu rahoto daga ofishin 'yan sanda na Santo. Cewa wasu bata-gari sun fada gidan Sunday Igboho da ke yankin Soka a Ibadan.

"Sun dinga harbe-harbe bayan isarsu gidan Sunday Igboho sanannu suka banka wuta ta babbake kadarorinsa. Har yanzu ba a yi kiyasin kudin kadarorin ba.

"Daga bisani an kashe wutar kuma na fara bincike a kan 'yan daban da suka yi wannan aika-aikar."

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna

A wani labari na daban, an saka 'yan majalisar jihar Kogi gaba da caccaka bayan zagayen jihohi da suka yi suna nemawa gwamna Yahaya Bello goyon baya daga jama'a domin fitowa takarar shugaban kasa a 2023.

'Yan majalisar da suka ziyarci Filato, Ebonyi da jihar Kogi, sun yi kira ga takwarorinsu da su goyi bayan Gwamna Bello idan 2023 ta iso.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, tunda har yanzu arewa ta tsakiya bata fitar da dan takarar shugaban kasa ba, akwai bukatar APC ta mika tikitinta ga Bello domin yayi takarar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel