Mutane 13 sun mutu a hadarin mota a Binuwai

Mutane 13 sun mutu a hadarin mota a Binuwai

- Mutane 13 sun rasa rayukan su sanadiyar wani mummunan hadarin mota a Ogudumu da ke Jihar Benue

- Daga cikin fasinjojin akwai uwa da yaran ta uku wanda suka rasa rayukan su nan take sai dai daga fasinjojin akwai wanda suka tsira

- Hukumar kiyaye afkuwar hadari ta kasa road safety ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana mutuwar mutane 12

Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukan su ranar Talata sanadiyar wani hadarin mota da ya faru a kauyen Ogudumu kan titin Otukpo-Adoka a karamar hukumar Otukpo da ke Jihar Benue.

Daily Trust ta ruwaito cewa daga cikin wanda suka rasa rayukan su akwai wata uwa da yayan ta uku wanda suka nufi Abuja cikin motar haya.

Mutane 13 sun motu a hadarin mota a Binuwai
Mutane 13 sun motu a hadarin mota a Binuwai. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji sun sada ƴan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe

Amma daga cikin mutanen da suka yi hadarin da safe, akwai wanda suka rayu.

Wani shaidar gani da ido ya ce motar wacce zata Abuja, tayi lodin fasinja daga garin Otukpo kuma ta fara tafiya lokacin da wata babbar tifa da ke zuwa daga daya bangaren ta daki motar, yayin da direban ya kasa sarrafa motar kuma ta kife a Ogudumu.

Wani wanda ya shaida lamarin ya ce sun mutu nan take saboda munin hadarin.

Da aka tuntube shi, babban kwamandan Road Safety (FRSC) na jihar, Mohammed Suleiman ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin mu ta wayar tarho.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Buhari ya naɗa Aghughu a matsayin sabon AGF

Ya ce hadarin, wanda ya afku sanadiyar karo tsakanin babbar tifa da mota kirar wagon, ya faru da misalin 10:45 na safe, ranar Talata tare da tabbatar da mutuwar mutane 12 yayin da shida ke asibiti suna karbar magani bayan sun ji raunika.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel