An kama matasa 'Hausawa' dauke da bindigu a Oyo

An kama matasa 'Hausawa' dauke da bindigu a Oyo

- Matasan garin Eruwa sun tare wata babbar mota dauke da maza da aka ce Hausawa ne da ke son shiga garin

- Matasan da aka tare dauke da bindigun farauta da wasu makaman sun ce za su tafi Eruwa ne domin yin farauta

- Sai dai matasan garin ba su gamsu da hakan ba hakan yasa suka mika matasan ga rundunar 'yan sandan jihar

Wasu matasa a unguwar Ido da ke Ibadan a Jihar Oyo, a ranar Litinin, sun kama wasu maza su 25 dauke da makamai da suka shigo garin a babbar mota wato roka.

Wakilin jaridar The Punch ya ruwaito cewa mazan da aka kama Hausawa ne don haka batun yasa matasan garin ke zargin su.

DUBA WANNAN: An cafke uba da ƴaƴan sa biyu a cikin gungun 'yan bindigan Katsina

An kama matasa 'Hausawa' dauke da makamai a Oyo
An kama matasa 'Hausawa' dauke da makamai a Oyo. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Mazan da aka gani tare da bindiga irin ta mafarauta sun ce suna hanyarsu ne ta zuwa yankin Eruwa a jihar domin yin farauta.

KU KARANTA: Wata mata ta sheƙawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi a Kano

Wata majiya ta ce bayan tare matasan an mika su hannun jamian rundunar 'yan sanda a jihar sannan ta kara da cewa matasan na Eruwa ba su amince sun shiga garin na su ba.

An ce an tafi da su headkwatar rundunar yan sanda da ke Eleyele a Ibadan domin zurfafa bincike.

Amma, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar Oyo, Mista Olugbenga Fadeyi ya ce ba shi da wata masaniya a kan lamarin a lokacin da aka nemi jin ba'asi daga gare shi.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel