Hisbah ta kama matasa shida da ke shirya casun baɗala a Bauchi

Hisbah ta kama matasa shida da ke shirya casun baɗala a Bauchi

- Hukumar Hisbah ta Jihar Bauchi ta kama matasa shida da laifin shirya casu na badala a gine-ginen makarantun frimare a jihar

- Hukumar ta gayyaci iyayen matasan ta basu shawarwari kana ta umurce su saka hannu kan takardar alkawarin ba za su sake ba

- Har wa yau hukumar ta yi kira ga gwamnatin jihar ta gaggauta kafa kwamitin masu gudanarwa da kuma kara ware wa hukumar kudaden gudanarwa

Hukumar Hisbah ta Jihar Bauchi ta ce ta kama matasa shida kan zarginsu da hannu wurin shirya casun 'badala' a kauyen Dolam da ke karamar hukumar Tafawa Balewa na jihar.

Aminu Idris, kwamishinan da ke kula da Hisbah da aiwatar da shari'a a jihar ne ya bayyana hakan yayin hira da kamfanin dillancin labarai NAN a ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

Hisbah ta kama wadanda suka shirya casun baɗala a Bauchi
Hisbah ta kama wadanda suka shirya casun baɗala a Bauchi. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An kama matasa 'Hausawa' dauke da bindigu a Oyo

Ya ce wadanda aka kama sun hada da Abdurrauf Kabir mai shekaru 25, Dabo Yusuf mai shekaru 26, Abdurrazak Isah mai shekaru 24, Habu Umar mai shakru 27, Yaron Nuhu-Maikaji, mai shekaru 30 da Abdurrashid Shehu mai shekaru 31.

Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin suna amfani da gine ginen makarantun firmare a jihar domin shirya irin wannan casun na badala.

Ya kara da cewa wadanda aka kama din sun saba shirya casu da ake yin rawan disco da aka kira 'Gwaidu' a inda suke aikata badala da 'yan mata.

A cewar Idris, bayan gano wannan aika-aikan da suka tafkawa, hukumarsa ta dauki mataki kuma ta yi nasarar kama su.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna)

Ya ce bayan bincike, hukumar ta Hisbah ta gayyaci iyayen wadanda aka kama ta basu shawarwari sannan ta saka su rattaba hannu kan takardar alkawarin ba za su sake ba.

Idris ya ce Hukumar ta Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba domin ganin ta gurfanar da duk wanda aka samu da irin wannan laifin a gaban kotu.

"A matsayi na na lauya, zan yi duk mai yiwuwa don ganin ba a saba dokokin mu ba," in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta yi gaggawan kafa kwamitin masu gudanarwa na Hukumar Hisbah na jihar kana da samar da karin kudade domin taimakawa hukumar gudanar da ayyukanta yadda ya dace.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel