Arangamar 'yan shi'a da 'yan sanda: An aike mutum daya lahira a Abuja

Arangamar 'yan shi'a da 'yan sanda: An aike mutum daya lahira a Abuja

- Mutum daya ya rasa ransa bayan arangamar 'yan shi'a da jami'an tsaro a Abuja, Najeriya

- Lamarin ya faru a ranar Talata a yankin Maitama kusa da ofishin hukumar kula da dan Adam

- Bayan fitowar 'yan shi'an, 'yan sanda sun dinga watsa barkonon tsohuwa tare da harbe-harbe

A kalla rai daya aka rasa yayin da wasu suka jigata a ranar Talata sakamakon arngamar 'yan sanda da 'yan kungiyar shi'a na Najeriya.

Lamarin ya faru a yankin Maitama da ke babban birnin tarayya da ke Abuja kusa da hukumar kula da hakkin dan Adam ta kasa.

A yayin da zanga-zangar tayi kamari, 'yan sandan sun dinga harbi tare da watsa barkonon tsohuwa domin tarwatsa 'yan shi'an, lamarin da ya kai ga kisan mutum daya a take.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane

Arangamar 'yan shi'a da 'yan sanda: An ji harbe-harben bindiga a Abuja
Arangamar 'yan shi'a da 'yan sanda: An ji harbe-harben bindiga a Abuja. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

An ga hayakin barkonon tsohuwa ya cika wurin yayin da karar harsasai suka cika iskar.

Shugaban kungiyar IMN, Abdullahi Mohammed, ya sanar da The Punch cewa mutane da yawa sun samu miyagun raunika.

Kamar yadda yace, nan ba da dadewa ba IMN za ta saki takarda a kan aukuwar lamarin. Duk kokarin tuntubar 'yan sanda da aka yi ya gagara.

KU KARANTA: Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya

A wani labari na daban, a ranar Laraba, gwamnatin jihar Kano ta fada wani gida wanda ake zargin masu garkuwa da mutane suna adana mutane idan sun sato su.

Premium Times ta ruwaito yadda a ranar Laraba 'yan sanda suka kwashe wasu masu garkuwa da mutane, ciki har da wata bazawara.

KNUPDA da jami'an tsaro sun kula da yadda bulldozer ta kwashe ginin tsaf dake Jaba a karamar hukumar Ungogo dake Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: