Farfesa Jega ya amsa tambaya akan kokarin Buhari a kan mulki
- Farfesa Attahiru Jega, stoho shugaban hukumar INEC, ya yi tsokaci akan kwazo da kokarin gwamnatin Buhari
- A cewar Farfesa Jega, gwamnatin Buhari ta bawa 'yan Nigeria da yawa mamaki kuma ta gaza fitar da su kunya
- A shekarar 2010 ne tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya fara nada Farfesa Jega a matsayin shugaban hukumar INEC
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfes Attahiru Jega, ya bayyana gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin ''babban abin takici."
Yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust, Jega ya ce gwamnatin Buhari ''ta gaza fitar da yawancin 'yan Nigeria kunya", kamar yadda TheCable ta wallafa.
Farfesa Jega ya rike hukumar INEC daga shekarar 2010 zuwa 2015, shekarar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya sha kaye a hannun Buhari.
KARANTA: Hare-hare akan makiyaya: Miyetti Allah ta bawa gwamnatin tarayya wata shawara a fusace
Tsohon shugaban kungiyar ASUU da Jami'ar BUK da ke Kano, Farfesa Jega ya kasance shugaban INEC na farko, kuma daya tilo har yanzu, da ya fara gudanar da manyan zabuka guda; a 2011 da 2015.
A cewar Farfesa Jega, duk da har yanzu 'yan Nigeria na yi wa Buhari fatan alheri, 'yan kasa suna cikin damuwa ''akan alkiblar da kasa ke dauka."
KARANTA: An kama soja da sabon shiga aikin dan sanda da laifin fashi da makami
"Buhari ya bawa mutane da yawa mamaki. Har yanzu yana da lokacin gyara al'amura idan zai iya hakan. Amma, maganar gaskiya, gwamnatin ta kasance babban abin takaici," kamar yadda Jega ya bayyana.
"An samu tabarbarewa al'amuran gwamnati a matakin tarayya da mafi yawan jihohi, hakan ne kuma yasa mu ke fama da kalubale a ko ina; yakin Boko Haram, 'yan bindiga, fashi da makami, da sauransu," a cewarsa.
Kalaman Farfesa Jega sun shiga sahun na saura manyan kasa irinsu tsohon shugaba Olusegun Obasanjo da Farfesa Wole Soyinka, wadanda suka dade da fara sukar gwamnatin Buhari.
Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.
A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a jihar Borno.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng