Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar

Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar

- Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da bude manyan makarantun gaba da sakandare na jihar a ranar Litinin

- Wannan na kunshe ne a wata takarda da ma'aikatar ilimin jihar ta fitar dauke da sa hannun babbar sakatariyar ma'aikatar

- Ta tabbatar da cewa dukkan makarantun da suka karya dokoki tare da hanyoyin dakile yaduwar annobar a jiharsa ta garkame su babu jan kunne

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bude makarantun gaba da sakandare na jihar a ranar Litinin, 25 ga watan Janairun 2021 a fadin jihar baki daya.

Amma kuma ta ja kunnen dukkan hukumomin makarantun da su kasance masu kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona da jihar ta Gindaya, Daily Trust ta tabbatar da hakan.

A wata takardar da ma'aikatar ilimi ta jihar ta fitar kuma ta samu sa hannun babbar sakatariyar ma'aikatar, Phoebi Sukai Yayi, an bayyana cewa wannan amincewar ta biyo bayan tura kungiyar dubawa tare da tantancewa dukkan makarantun gaba da sakandare na jihar, wadanda suka tabbatar da cewa makarantun sun shirya kuma sun kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a fadin jihar.

DUBA WANNAN: Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya

Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar
Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan umarnin daga gwamnatin jihar ya biyo baya ne sa'o'i kadan bayan jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta sanar da cewa ba za ta iya cigaba da shirin bude makarantar ba a ranar 25 ga watan Janairun 2020 saboda tana jiran umarni daga gwamnatin jihar.

Daraktan sashen hulda da jama'a na jami'ar, Auwalu Umar tun farko ya ce gwamnatin jihar ta turo kungiyar tamtancewa a ranar 20 ga watan Janairun 2021 domin duba yadda makarantar ta shirya kiyaye dokokin dakile yaduwar mugunyar annobar.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane

Amma kuma, takarda da ta fito daga ma'aikatar ilimin jihar a yammacin ranar Lahadi ta ce: "Dukkan matakan da muka duba kuma muka tabbatar an shirya dole ne a kiyayesu. Rashin hakan zai sa a sake garkame duk makarantar da ta take ba tare da bata lokaci ba."

"Komawar dukkan makarantun gaba da sakandare zai kasance a rarrabe ne kamar yadda makarantun suka tanadar da kuma yadda suka tsara," takardar tace.

Kamar yadda ma'aikatar ta sanar, babu sanarwa za ta dinga kai ziyara manyan makarantun gaba da sakandaren jihar domin tabbatar da cewa ana bin dokar kiyaye yaduwar annobar korona.

A wani labari na daban, a ranar Alhamis rundunar sojin Najeriya tace tana samun nasarori, kuma tana dab da kawo karshen ta'addanci da rashin tsaro a kasar nan.

Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wani taro a Abuja.

Enenche ya bayar da misalin yadda suka ci karfin ta'addanci a jihar Zamfara da Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ngng

Asali: Legit.ng

Online view pixel