Haba, Malam Sani: Auren dattijo da matashiyar budurwa ya yamutsa hazo

Haba, Malam Sani: Auren dattijo da matashiyar budurwa ya yamutsa hazo

- Auren wani dattijo mai suna Malam Sani da wata matashiyar budurwa ya girgiza yanar gizo tare da haddasa cece-kuce

- Dumbin jama'a da suka bayyana ra'ayinsu sun bayyana rashin dacewar irin wannan hadin aure a tsakanin dattijo da matashiya

- Wasu daga cikin masu bayyana ra'ayinsu sun bukaci a kama duk wani mai hannu a kulla auren Malam Sani

Wani aure da aka daura tsakanin wani dattijo mai suna Malam Sani da wata matashiyar budurwa ya yamutsa hazo tare da girgiza dandalin sada zumunta.

A ranar Litinin ne hotunan bikin Malam Sani da matashiyar suka bayyana a dandalin sada zumunta na Tuwita, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Rubutun da ke jikin jakar kayan tsarabar da aka bawa wadanda suka halarci wurin taron bikin Malam Sani da matashiyar ya nuna cewa an daura auren ne a ranar 22 ga watan Janairu, 2021.

A jikin jakar akwai hoton Malam Sani da farin gemunsa yayin da matashiyar amaryarsa ke tsaye a gefansa, a salo da yanayin hotunan matasa na kafin biki.

Sai dai, hoton bikin ya girgiza yanar gizo tare da yamutsa saboda banbancin shekarun da ke tsakanin ma'auratan kamar yadda za'a iya gani.

Haba, Malam Sani: Auren dattijo da matashiyar budurwa ya yamutsa hazo
Haba, Malam Sani: Auren dattijo da matashiyar budurwa ya yamutsa hazo @TheCable
Asali: Twitter

Jama'a sun bayyana mabanbantan ra'ayi tare da nuna fushinsu da kuma yin tambaya akan halaccin irin wannan aure.

Wani mai suna Usman Okai Austin ya bayyana cewa; "Habba Mallam Sani....ko kadan baka kyauta ba, bai kamata a bar irin haka ta ke faruwa ba."

Ita kuwa wata mai suna Aisha Abdullahi cewa ta yi; "kamata ya yi a ce wannan yarinyar tana makaranta, ya kamata a kama duk wasu masu hannu a kulla auren."

Wani mai suna Quame cewa ya yi; "Mallam Sani ba ya jin kunya. Ya nuna wauta da rashin dattako, eh, haka na fada.

Wasu daga cikin wadanda suka yi martani sun bayyana cewa daga gani Malam Sani zai iya yin jika da yarinyar da ya aura.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel