Bidiyon saurayi da abokansa suna jibgar budurwarsa bayan sun kama ta da kato

Bidiyon saurayi da abokansa suna jibgar budurwarsa bayan sun kama ta da kato

- Bidiyon wasu matasa suna jibgar wata budurwa ya janyo cece-kuce daga jama'a

- Kamar yadda aka gano, saurayin da abokansa suna dukanta ne saboda cin amana

- Sun kama budurwar tana cin amanar saurayin da wani gardi na daban

Wani bidiyo mai cike da bada mamaki ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani. A bidiyon, an saurayi yana dukan budurwarsa yayin da abokansa suke taya shi jibgarta.

Kamar yadda aka gano kuma bidiyon ya bayyana, budurwar ta ci amanar saurayin nata ne da wani saurayin na daban.

A bidiyon, an ga budurwar tana ihun neman dauki yayin da kattin maza ke ta dukanta.

Babu shakka bidiyon ya samu kushe tare da Allah wadai daga jama'a da suka kalla.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Majalisa ba za ta yaki Buhari ba saboda son farantawa wasu rai, Lawan

Bidiyon saurayi da abokansa suna jibgar budurwarsa bayan sun kama ta da kato
Bidiyon saurayi da abokansa suna jibgar budurwarsa bayan sun kama ta da kato. Hoto daga Lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

KU KARANTA: Dattawan arewa sun bukaci makiyaya da su yi watsi da umarnin Akeredolu

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Daily Trust ta wallafa.

An kama daya daga cikin ma'aikatan tsaro na jami'ar mai suna Aliyu Abubakar sakamakon bai wa masu garkuwa da mutanen tallafi a dukkan lokutan da suke sace jama'a a jami'ar.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, CP Frank Mba, ya sanar da damke wani Malam Jafaru da ke samar da asiri ga masu garkuwa da mutanen.

Tun a karshen shekarar da ta gabata ne masu garkuwa da mutane suka dinga sace farfesoshi da ke zama a cikin rukunin gidajen malaman jami'ar.

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne masu da mutanesaka sace Farfesa Bako.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng