Bazan iya jiran miji na ya fito daga kurkuku ba, matar aure da shaidawa kotu
- Wata mata da aka garkame mijin ta a kurkuku ta bukaci kotu ta raba auren su saboda ba zata iya jira ya fito ba
- Matar wadda tace tun da fari an mata karyar lokacin da mijin ta zai shafe a kurkuku, bata son sabawa Allah kafin a sallami mijin nata
- Alkalin kotun da ke zamanta a Kasuwar Nama, Jos ya raba auren kamar yadda matar ta bukata
Wata kotu a Jos, da ke zamanta a Kasuwan Nama, ranar Alhamis, ta raba wani aure tsakanin Rakaiya Abdullahi da mijin ta, Saleh Adam bayan ta zargi mijin nata da yaudarar ta, The Nation ta ruwaito.
NAN ta ruwaito cewa mai korafi, Rakaiya, mai haihuwa daya, ta bukaci a sake ta, ta ce da mijin ta da waliyin sa, Sale Borno, sun yi mata karya akan garkame mijin nata.
DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa
Ta shaidawa kotun cewa duka wanda tayi karar sun yaudareta akan ta ci gaba da zaman aure bayan an kama mijin nata da laifi kuma an kai shi kurkuku a bisa laifin da ba a bayyana ba.
Matar ta ce ta yanke shawarar zama bayan wanda ake kara na biyu, Borno yayi mata karyar mijin ta zai shafe shekara uku kacal.
Ta sake shaidawa kotun cewa sai bayan da shekara uku ta cika sai waliyin mijin nata ya shaida mata cewa shekara bakwai aka daure mijin nata takamaimai.
KU KARANTA: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam
Rakaiya ta roki kotun da ta karbi rokon ta, ta raba auren saboda bata son sabawa Allah kafin a saki mijin nata daga kurkuku.
Alkalin kotun, Sulaiman Lawal, ya raba auren kamar yadda mai korafin ta bukata.
A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng