2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja (Hotuna)

2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja (Hotuna)

- Fastocin takarar shugabancin kasa na gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike sun bayyana a Abuja

- An lika su a wuraren da kowa zai iya gani a kan titin Herbert Macaulay a tsakiyar birnin Abuja

- Ana hasashen Wike zai dauki gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a matsayin mataimakinsa indai takarar ta tabbata

Fastocin yakin neman zaben Shugabancin kasa dauke da hoto da sunan gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, suna yawo a babban birnin tarayya, Abuja, The Punch ta ruwaito.

Wike, dan jam'iyyar PDP, yana wa'adin sa na biyu kuma na karshe a matsayin gwamnan jihar ta kudu maso kudanci.

Wakilin mu ya ga fastocin wanda iri biyu ne a Abuja da safiyar Litinin.

2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayana a Abuja (Hotuna)
2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayana a Abuja (Hotuna). Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa

An lika su a wuraren da kowa zai iya gani a kan titin Herbert Macaulay a tsakiyar birnin Abuja.

An ga wasu like a jikin ginin katangar ofishin yakin neman zabe Buhari/Osinbajo a shekarar 2015 da 2019.

An lika wasu fastocin a kusa da hedikwatar NNPC da kuma katangar da ke kallon Nigerian Defence College da aka fi sani da War College.

Taken da aka rubuta a saman fastar shi ne "A ceci Najeriya 2023", shugaban kungiyar a ceci Najeriya, Jingiri Bala Mato ne ya dauki nauyi.

2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayana a Abuja (Hotuna)
2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayana a Abuja (Hotuna). Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Fastocin na dauke da tambarin PDP da, "A ceto Najeriya daga rashin tsaro, talauci, kashe kashen yan bindiga. Mu goya wa Chief Barr Nyesom Wike don zama shugaba kasa, a tarrayyar Najeriya 2023."

Wikilin mu ya lura da yadda aka rubuta sunan gwamnan, Nyesom, aka mayar da shi "Nyemsom" a duka nau'in fastocin biyu.

KU KARANTA: Jerin manyan kyaututuka masu tsada 10 da aka yi wa Donald Trump

Daya daga cikin fastocin na dauke da hoton gwamnan cikin shigar yankin kudu maso kudu da hular kaboyi, a dayar kuma cikin shigar arewa sanye da hula.

Ana tsammanin Wike da Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto za su hade kai don samun tikitin takarar Shugabancin kasar a 2023.

2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayana a Abuja (Hotuna)
2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayana a Abuja (Hotuna). Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Tambuwal, wanda shi ma ke wa'adin sa na karshe na gwamna a jam'iyyar PDP na daya daga cikin wanda Wike ke gayyata don kaddamar da ayyuka a baya bayan nan.

Ya nemi takarar Shugabancin kasa, sai dai Atiku ya kada shi a zaben fidda gwani.

Tambuwal ya samu goyon bayan Wike a zaben da aka gudanar a Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers.

A satin da ya gabata Wike ya bukaci a bada miliyan 500 ga wanda iftila'in gobara ya shafa a Jihar Sokoto.

Batun da ya janyo wa ma gwamnan cecekuce daga jam'iyyar adawa da wasu mutane.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel