Buhari bai san me yake faruwa a jam'iyya ba; Rochas ya yi karin haske akan zamansa a APC

Buhari bai san me yake faruwa a jam'iyya ba; Rochas ya yi karin haske akan zamansa a APC

- Rochas Okorocha, tsohon gwanan jihar Imo, ya ce har yanzu yana nan daram a cikin jam'iyyar APC

- A makon jiya ne toshon gwamnan wanda yanzu sanata ne a jam'iyyar APC ya sanar da cewa suna shirin kafa sabuwar jam'iyyar gabanin zaben 2023

- A cewar Rochas, wasu 'yan kanzagi sun shigo APc tare da kankane komai, kuma shugaba Buhari bai san wainar da ake toya ba a jam'iyyar

A ranar Asabar ne aka ji tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, na jaddada cewa har yanzu yana nan cikin jam'iyyarsa ta APC duk kuwa da rikicin da ya dabaibaye ta har su ke yunkurin kafa sabuwar jam'iyya.

Okorocha ya yi wannan furuci ne loƙacin da ya ke yiwa kwamatin riƙo na jam'iyya jawabi a Owerri, babban birnin jihar Imo, inda ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai san wainar da ake soya ba a cikin APC.

Okorocha, wanda ke wakiltar mazaɓar Imo ta yamma a zauren majalisar dattijai, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu da ba asalin ƴan jam'iyyar ba suke neman kankane komai, sai yadda suka yi da komai.

KARANTA: Hare-hare akan makiyaya: Miyetti Allah ta bawa gwamnatin tarayya shawara a fusace

Tsohon gwamnan, ya musanta raɗe-raɗin da ake na cewa yana shirin barin jam'iyyar sakamakon rikicin da ya dabaibayeta a jiharsa ta Imo, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

Buhari bai san me yake faruwa a jam'iyya ba; Rochas ya yi karin haske akan zamansa a APC
Buhari bai san me yake faruwa a jam'iyya ba; Rochas ya yi karin haske akan zamansa a APC
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya bayyana ƙudurinsa na kafa wata sabuwar tafiyar siyasa dangane da zaɓen 2023 dake ƙaratowa.

Okorocha ya ce, akwai akwai waɗanda aka kafa jam'iyya da su waɗanda sun fi ƙarfin a kore su a matakin jiha ko na ƙasa baki ɗaya.

KARANTA: An kama soja da sabon shiga aikin dan sanda da laifin fashi da makami

"Jam'iyyata, har yanzu, ita ce APC. Kar ku rikice don na ce akwai mutanen ƙwarai da na banza cikin jamiyyar APC da PDP da ya kamata su haɗa kai don cigaban ƙasar nan. Ina magana ne kan gwagwarmaya ba jam'iyya ba"

"Ban bar APC ba, ina nan cikinta. Ba wanda ya fi ni ta cewa a APC. Na sha mafi munin zagi a yankin kudu maso gabas a 2015 akan Buhari, Tinubu, ni kaina da wasu mutanen.

"Amma wasu daga baya su zo da niyyar karɓe ragamar jam'iyyar baki ɗaya." in ji shi.

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin ''babban abin takaici."

Yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust, Jega ya ce gwamnatin Buhari ''ta gaza fitar da yawancin 'yan Nigeria kunya", kamar yadda TheCable ta wallafa.

Farfesa Jega ya rike hukumar INEC daga shekarar 2010 zuwa 2015, shekarar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya sha kaye a hannun Buhari.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel