An kama soja da sabon shiga aikin dan sanda da laifin fashi da makami
- Wani sabon shiga aikin dan sanda tare da wani soja sun shiga hannu bisa zarginsu da laifin fashi da makami a jihar Ondo
- Kwamishinan 'yan sanda jihar Ondo ne ya gabatar da jami'an tsaron a cikin sauran masu laifi da aka yi holinsu a hedikwatar 'yan sanda
- Sai dai, jami'in rundunar sojin ya musanta zargin da ake yi masa tare da bayyana cewa babu hannunsa a cikin laifukan
An kama wani soja, Innocent Victor, da wani sabon shiga aikin dan sanda, David Friday, da aikata laifin fashi da makami a jihar Ondo.
Friday yana aiki ne a ofishin rundunar 'yan sandan Nigeria na karamar Idanre yayin da Victor ke aiki a bataliyar rundunar soji ta 32 da ke Owena.
Ana zargin jami'an tsaron biyu da amfani da makamai masu hatsari wajen yi wa jama'a fashi a Akure, babban birnin jihar Ondo, kamar yadda Punch ta rawaito.
Da ya ke holin masu laifin a hedikwatar rundunar 'yan sandan jiha, kwamishinan 'yan sanda Ondo, Bolaji Salami, ya ce an taba zargin David da satar Babur.
A cewar kwamishinan, a baya an taba shigar da korafin bacewar wani Babur a wurin aikin David.
KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria
Daga cikin kayan da kwamishinan ya lissafa cewa an samu a wurin masu laifin sun hada da N6000, wayar hannu da darajarta ta kai N8,500, man fetur lita 30 da kudi N125,000.
Sai dai, jami'in rundunar sojin ya musanta zargin da ake yi masa tare da bayyana cewa ya janye jikinsa daga wurin aikata laifin.
A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke Malam Ibrahim Tukur, mataimakin shugaban makarantar sakandire, bisa zarginsa da yi wa daya daga cikin dalibansa ciki.
An kama Malam Ibrahim ne bayan dalibar da ya yi wa ciki, mai shekaru goma sha biyu, ta haihu, amma ta hanyar yi mata tiyatar zaro jariri.
A ranar Laraba ne rundunar 'yan sanda ta yi holin masu laifuka daban-daban, cikinsu har da Malam Ibrahim.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng