Wani gwamnan Nigeria zai mutu, shahararren fasto ya yi gargadi a wahayin 2021
- Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi hasashen abubuwan da yayi ikirarin za su faru a 2021
- Shugaban addinin ya yi ikirari cewa wasu gagaruman abubuwa za su wakana a siyasan Najeriya
- Okikijesu ya fada ma jama’a dalilin da yasa akwai bukatar su yi wa kujerar mulkin Najeriya addu’a
Wani Shugaban addini, Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi ikirarin cewa Allah ya bayyana masa cewa wani gwamnan Najeriya zai mutu a 2021.
Okikijesu wanda yayi ikirarin a wani wahayi da ya saki na sabuwar shekaara ya ce mutuwar gwamnan namiji zai ba mace damar zama gwamna.
KU KARANTA KUMA: Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji
Ya ce:
“Haka Ubangiji ya fadi: Wata mace za ta zama Gwamna kwanan nan. Wani gwamna namiji zai mutu kuma mataimakiyarsa wace take mace za ta dare kujerarsa a matsayin gwamna.
“Haka Ubangiji ya ce: Za su amince ccewa mace wacce ta kasance mataimakiyar gwamna ta zama gwamnan wucin gadi. Zai zama kamar irin lamarin Jonathan da Yar’adua.”
Sai dai malamin bai bayyana jihar Najeriya da hasashensa zai fada a kai ba.
Ya kuma yi ikirarin cwa Allah ya bayyana masa cewa za a yi gagarumin rikici a Aso Rock.
A cewarsa, rikcin zai jijjiga kasar gaba daya kuma zai shafi duk wani ruhi da ke kasar.
Okikijesu ya ce:
“Ubangiji ya fadi cewa: Wani gagarumin rikici zai barke a Aso Rock tsakanin Janairu da Maris 2021. Zai bazu sosai; zai girgiza kasar sannan ya sa mutane rawar jiki."
KU KARANTA KUMA: Matasan arewa sun saki jerin sunayen yan siyasan da za su marawa baya don zama Shugaban kasa a 2023
Ya bayyana cewa rikicin da zai faru a fadar Shugaban kasa zai sanya mutane cikin damuwa. Malamin ya bukaci al’umman kasar da su yiwa Aso Rock addu’a.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Juma'a ya bayyana cewa domin adalci, ya kamata mulki ya koma kudu a shekarar 2023.
Ya soki maganganin cewa idan aka baiwa wani sashen kasar nan mulki zasu yi kokarin ballewa daga kasar.
Ya jaddada cewa akwai bukatar nuna adalci, saboda mayar da wani bangare saniyar ware ya sa suke neman ballewa daga kasa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng