Amaechi: A miliyan ₦900 aka kulla kwangilar shafin sayen tikitin jirgin kasa

Amaechi: A miliyan ₦900 aka kulla kwangilar shafin sayen tikitin jirgin kasa

- A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da bude shafin yanar gizo domin sayen tikitin jirgin kasa a tashoshin Abuja da Kaduna

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce akan miliyan dari tara gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar aikin

- A cewar Amaechi, kamfanin da ya hada gwuiwa da FG; SecureID Limited, zai damka shafin a hannun hukumar NRC bayan shekara goma

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa akan Naira miliyan dari tara (N900,000,000) gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar samar da shafin yanar gizo domin sayen tikitin jirgin kasa.

Amaechi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da shafin wanda zai koma hannun hukumar kula da jiragen kasa bayan shekara goma.

KARANTA: Farfesa Wole Soyinka: Na yafewa Amurkawan da suka zabi Trump, yanzu zan iya komawa Amurka

A cewar ministan, an damka kula da gudanar da shafin yanar gizon a hannun wani kamfani kafin daga bisani ya mayar da shafin hannun hukumar NRC.

Amaechi: A miliyan ₦900 aka bayar da kwangilar shafin sayen tikitin jirgin kasa
Amaechi: A miliyan ₦900 aka bayar da kwangilar shafin sayen tikitin jirgin kasa
Source: Twitter

KARANTA: Katsina: An cafke mataimakin shugaban makarantar sakandire saboda yi wa daliba 'yar 12 ciki

"Wannan aiki ne na hadin gwuiwa a tsakanin NRC, NITDA, bayan samun sahalewar gwamnatin tarayya, Kuma an fara tsara kirkirar shafin tun shekaru uku da suka gabata.

"Yau rana ce mai muhimmanci da muka kaddamar da tsarin siyen tikitin jirgi ta yanar gizo a tashoshin jiragen kasa a tsakanin Abuja da Kaduna. Za'a kara fito da wasu tsaruka a shafin domin jin dadin jama'a.

Ministan ya godewa kamfanin SecureID Limited wanda ya bayyana cewa ya bayar da muhimmiyar gudunmawa kuma zai cigaba da inganta shafin domin jin dadin masu sufuri ta jiragen kasa.

Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya, a ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, 2021, ta rattaba hannu akan bayar da kwagilar gina titin jirgin kasa na zamani daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar da kuma daga Kano zuwa Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Kamfanin da aka bawa kwangilar aikin, Mota-Engil Group, ya dauki alkawarin ginawa Nigeria Jami'a kyauta kafin kammala kwangilar da aka bashi.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya sanar da hakan yayin da ya wallfa hotunansa yayin saka hannu akan kwangilar a shafinsa na dandalin sada zumunta.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel