Siyan rigakafin korona na N400bn: Abinda bai dace ba ake ba wa fifiko, Bafarawa
- A jiya Laraba tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya nuna takaicinsa akan zunzurutun kudin da aka shaka wa PTF
- Bafarawa ya ce N400,000,000 da 'yan majalisar tarayya suka ware wa PTF na riga-kafin COVID-19 sun yi yawa
- 'Yan Najeriya suna da matsaloli na tsaro, garkuwa da mutane da sauransu wadanda ya kamata a yi amfani da kudin wurin kulawa da su
A jiya ne tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, yace N400,000,000,000 da majalisar tarayya ta amince wa reshen PTF na kula da COVID-19 ya yi yawa.
A cewarsa, ware wannan sununun dukiyar wurin siyan allurar riga-kafin cutar ya yi yawa, akwai abubuwa masu muhimmanci da kasa take bukata da suka fi wannan, Vanguard ta ruwaito.
A cewarsa, me zai hana a yi amfani da dukiyar wurin gyara matsalolin tsaro, ta'addanci da garkuwa da mutane dake addabar Najeriya?
KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke jami'in tsaron ABU da ke taimakawa masu garkuwa da mutane
Bafarawa ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai akan matsalolin tsaro da kuma cutar COVID-19.
Ya bukaci PTF da ta gabatar kuma ta bayyana yadda za tayi da N3,500,000,000 su shige zuruf cikin shirin riga-kafin cutar COVID-19, da kuma siyayyar da suka yi da kudaden.
'Yan Najeriya suna bukatar sanin yadda N3,500,000,000 suka shige, ba wai su dinga jin ana kiran zunzurutun kudade ba.
Kamar yadda yace, kaso 60 bisa 100 na 'yan Najeriya basu yarda da cutar COVID-19 ba, amma kuma an tattara uwar dukiya an shaka wa PTF don samar da riga-kafin cutar.
KU KARANTA: Saurayi ya biya kudin abincinsa shi kadai bayan budurwa ta je mishi da kawaye 2
A wani labari na daban, shugaban kungiyar dattawan arewa ya dakatar da makiyayan jihar Ondo daga barin mahallinsu kuma kada su yarda a dinga siffantasu da 'yan ta'adda kuma masu laifi.
A wata takarda ta ranar Laraba, Hakeem Baba-Ahmed, kakakin kungiyar ya umarci Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, da ya ajiye batun bai wa makiyayan jiharsa lokaci na su tattara ya nasu ya nasu su bar dajikan dake jiharsa.
Ya bayyana gwamnan a matsayin wanda ba ya taimako kuma macuci, The Cable ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng