Mayakan Boko Haram basu samu galaba akan sojoji ba; DHQ ta magantu akan harin Marte

Mayakan Boko Haram basu samu galaba akan sojoji ba; DHQ ta magantu akan harin Marte

- Hedikwatar rundunar tsaro ta musanta rahotannin wasu kafafen yada labarai akan harin Marte da ke jihar Borno

- A makon da ya gabata ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji da ke wajen garin Marte

- Janar John Enenche ya ce akarun soji ne suka samu nasara akan 'yan ta'addar sabanin rahoton cewa an samu galaba akansu

Hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta musanta rahotannin kafafen yada labaran da suka bayyana cewa an samu galaba akan rundunar sojin Najeriya yayi harin garin Marte.

A ranar 15 da 16 ga watan Janairu ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

Janar John Enenche, shugaban sashen yada labari na rundunar tsaro ta kasa, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram/ISWAP sun kai farmaki sansanin soji da ke wajen garin Marte, amma an dakile harin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito Enenche na cewa dakarun soji sun kashe dumbin mayakan tare motocinsu na yaki guda 13.

KARANTA: Katsina: An cafke mataimakin shugaban makarantar sakandire saboda yi wa daliba 'yar 12 ciki

"Wasu labarai na nuna Kamar an murkushe dakarun soji yayin harin, wanda hakan ba gaskiya bane.

"Sun fara kaddamar da harin ne ta wani shingen binciken ababen hawa da ke kusa da wani gidan mai.

Mayakan Boko Haram basu samu galaba akan sojoji ba; DHQ ta magantu akan harin Marte
Mayakan Boko Haram basu samu galaba akan sojoji ba; DHQ ta magantu akan harin Marte
Asali: Twitter

"Dakarun soji da ke wurin dole su janye jikinsu kamar yadda aka koya musu a dabarun yaki.

"Ba guduwa suka yi ba, sun yi hakan ne da gan-gan domin zuko 'yan ta'addar zuwa wurin da za'a yi musu rubdugu.

KARANTA: Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Teti, shekara 2,500 baya

"Kuma hakan ce ta faru a lokacin, sun fada tarko, don kafin su ankara tuni sojoji sun sanar da sojojin sama domin kawo musu agaji.

"An kashe da dama daga cikin 'yan ta'addar tare da lalata motocinsu na yaki guda 13 a karshen harin da suka kai ranar," a cewarsa.

Enenche ya bayyana cewa rundunar soji ta matukar kassara 'yan ta'adda a jihar Borno domin yanzu basu da katabus kamar yadda suke da shi a baya.

Legit.ng ta rawaito cewa a ranar Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa rundunar jami'an tsaro ta 'Thunder Srike' ta kaddamar da harin kwanton bauna akan wasu 'yan bindiga a yankin karamar hukumar Kagarko.

Mista Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, ya sanar da cewa jami'an tsaro sun kashe biyu daga cikin 'yan bindigar a cikin jawabin da ya fitar.

A cewar Aruwan, rundunar jami'an tsaro ta samu nasarar kaddamar da harin ne a daren ranar Litinin a kan hanyar Sabon Iche zuwa Kagarko.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng