Gwamnan Bauchi ya gana da Atiku a Dubai yayinda aka fara tattauna batun 2023

Gwamnan Bauchi ya gana da Atiku a Dubai yayinda aka fara tattauna batun 2023

- Wani ganawa da aka yi tsakanin manyan yan biyu daga arewa maso gabas ya sa ana rade-radi

- Gwamna Bala Mohammed ya ziyarci Alhaji Atiku Abubakar a Dubai kwanan nan

- Masu sanya idanu a harkokin siyasa sun ce ganawar ba zai rasa nasaba da kudirin shugabannin biyu ba a zaben 2023

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ziyarci tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a karshen makon da ya gabata, lamarin ya haddasa rade-radi kan ganawar shugabannin biyu.

Atiku, dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, ya shafe tsawon lokaci a katafaren gidansa da ke Dubai, hakan ya sa makusantansa da dama a Najeriya zuwa daular Larabawan don ganawa shi.

Gwamna Mohammed ya kasance daya daga cikin makusantan tsohon mataimakin Shugaban kasar da suka ziyarce shi kuma masu lura da harkar siyasa sun ce akwai wata a kasa.

Gwamnan Bauchi ya gana da Atiku a Dubai yayinda aka fara tattauna batun 2023
Gwamnan Bauchi ya gana da Atiku a Dubai yayinda aka fara tattauna batun 2023 Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Gwamnan ya samu rakiyan Shugaban jam’iyyar PDP na jihar kuma tsohon sakataren gwamnati, Barista Ahmad Ibrahim Dandija.

KU KARANTA KUMA: Kwantan ɓauna: Yan bindiga sun kashe jami'an sa-kai 7 a Niger

Kasancewar Dandija a ganawar, ya sa ana ta rade-radi a shafin soshiyal midiya cewa ganawar baya rasa nasaba da zaben 2023.

Sun yi ganawar ne yan kwanaki bayan wata kungiyar arewa, Northern Youth Leaders Forum (NYLF), ta bayyana sunayen yan siyasan da take duba yiwuwar marawa bayan zama Shugaban kasa a 2023.

An ambaci Gwamna Mohammed da Atiku cikin jerin sunayen bayan kungiyar ta kaddamar da cewa yan takara daga arewa maso gabas kadai za ta marawa baya.

Babu tabbacin ko Gwamna Mohammed na da ra’ayin neman takarar Shugaban kasa a 2023, domin dai yana a zangonsa na farko ne a matsayin gwamnan jihar Bauchi.

KU KARANTA KUMA: A daina yi wa makiyaya kudin goro, suna da yancin zama a duk inda suke so, Shehu Sani ga Akeredolu

A daya bangaren kuwa da alama Atiku na da ra’ayin takara kuma da daman a ganin wannan ne karo na karshe da zai nemi kujerar.

A wani labari, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwararsa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

A ziyarar, Wike ya baiwa gwamnatin jihar gudunmuwar milyan dari biyar domin sake gina kasuwar.

Hakazalika ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel