Ban yarda da ita ba; Yahaya Bello ya gargadi 'yan Nigeria akan rigakafin Korona

Ban yarda da ita ba; Yahaya Bello ya gargadi 'yan Nigeria akan rigakafin Korona

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fito fili karara ya soki rigakafain allurar kwayar cutar korona

- A cewar gwamnan, me yasa har yanzu ba'a samu rigakafin HIV da sauran wasu dumbin cututtuka da suka addabi jama'a ba

- Bello ya yi kaurin suna wajen suka tare da kin yin biyayya ga matakan da gwamnati ke dauka akan annobar korona

Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi, ya nuna shakku akan rigakafin annobar korona tare da yin zargin cewa za'a yi amfani da ita domin hallaka jama'a.

Nigeria, kamar sauran kasashen duniya, na fuskantar hauhawar alkaluman mutanen da ke kamuwa da kwayar cutar bayan dawowar annobar a karo na biyu.

Tuni gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta sayi rigakafin korona wacce za'a fara yi wa 'yan Nigeria kyauta da zarar ta iso a karshen watan Janairu.

Shugabannin duniya da suka hada da Joe Biden, Benjamin Netanyahu, Firaministan Daular Larabawa, da sauransu sun karbi allurar rigakafin kamar yadda aka nuna kai tsaye a gidajen talabijin.

KARANTA: An kama matar dan bindigar Zamfara a cikin masu garkuwa da mutane a Kano

Sai dai, duk da hakan, Yahaya Bello ya yi watsi da allurar rigakafin yana mai fadin cewa za'a yi amfani da ita wajen hallaka jama'a.

Yahaya Bello ya soki allurar rigakafin ne a gaban taron jama'a kamar yadda jaridar TheCable ta bayyana tare da yin ikirarin mallakar faifan bidiyon Kalaman gwamnan.

Ban yarda da ita ba; Yahaya Bello ya gargadi 'yan Nigeria akan rigakafin Korona
Ban yarda da ita ba; Yahaya Bello ya gargadi 'yan Nigeria akan rigakafin Korona
Asali: Twitter

"An ce an kirkiro rigakafin kwayar cutar korona a cikin kasa da shekara daya, amma har yanzu babu rigakafin kwayar cutar HIV da zazzabin cizon sauro da sauran dumbin cututtuka da suka addabi jama'a.

"Suna son yin amfani da sunan allurar rigakafi domin sakawa jama'a ciwon da zai kashe ku da mu baki daya. Allah dai ya sawwake," a cewarsa.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Sannan ya cigaba da cewa; "ya kamata mu tuna abin da ya taba faruwa a baya, lokacin da kamfanin Pfizer ya yi gwajin allurar rigakafi a Kano, wanda hakan ya yi sanadiyyar gurguncewar yara da yawa. Ai mun koyi darasi.

"Idan sun ce za'a yi musu kuma a nuna kai tsaye a akwatin talabijin, babu damuwa, ra'ayinsu ne.

"Kar ku ce na hana a yi muku allurar rigakafin amma dai ina shawartarku da ku bude idanuwanku sosai kafin karbar allurar."

Wannan ba shine karon farko da Bello ya fara musantawa tare da karyata wasu bayanai dangane da cutar korona ba.

Gwamnan ba ruwansa da dokar nesanta balle batun saka takunkumin fuska a duk lokacin da za'a gan shi a wurin taro hatta da abokansa gwamnoni.

A makon da ya gabata ne Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sabunta sharudan da makarantu zasu cika da matakan da zasu dauka bayan sun bude a ranar 18 ga watan Janairu.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu, ya sanar da cewa za'a bude makarantu kamar yadda aka tsara.

Ana shawartar Malamai su tabbatar dalibai sun nesanta da juna a ajuzuwansu tare da tilasta biyayya ga dukkan matakan kare kai.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel