Tsofaffin gwamnoni na shirin ƙirƙirar sabuwar babbar jam'iyyar haɗaka

Tsofaffin gwamnoni na shirin ƙirƙirar sabuwar babbar jam'iyyar haɗaka

- Tsofin gwamnoni da gwamnoni masu ci a jam'iyyun APC da PDP sun fara kokawar siyasa akan zaben 2023

- An samu rabuwar kai da banbancin ra'ayoyi da fahimta akan yadda za'a tunkari zabe na gaba a kasa

- Rochas Okorocha, sanata kuma tsohon gwamnan APC, ya ce babu gudu, babu ja da baya a batun kirkrar sabuwar jam'iyya

Wasu gwamnoni masu ci da kuma tsofaffi daga manyan jam'iyyu biyu na APC da PDP na shirye shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, kamar yadda gamsassun majiyoyin siyasa suka fara bayyanawa a karshen mako.

A ɗaya ɓangaren kuma akwai gwamnonin da suketa aiki tuƙuru da zummar ganin waye ya kamata ya zama nagartaccen ɗan takarar Shugaban ƙasa a 2023 a dukkanin jam'iyyu biyu.

Sai kuma tsofaffin gwamnoni wanda suka haɗe kansu don a cigaba da damawa da su cikin al'amuran siyasa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa tuni gwamnoni suka fara tuntuɓa akan ƙirƙirar jam'iyyar haɗin guiwa daga manyan jam'iyyu biyu, kamar yadda Sanata Rochas Okorocha, tsohon gwamnan Imo ya tabbatar.

Tsofaffin gwamnoni na shirin ƙirƙirar sabuwar babbar jam'iyyar haɗaka
Tsofaffin gwamnoni na shirin ƙirƙirar sabuwar babbar jam'iyyar haɗaka
Asali: Twitter

Tsofaffin gwamnoni suna tuntuɓar wasu gwamnoni masu ci don zawarto su cikin jam'iyyar da suke shirin ƙirƙira.

Sai dai ba'a bayyana bayanan jam'iyyar da ake shirin ƙirƙira ba.

KARANTA: An kama matar dan bindigar Zamfara a cikin masu garkuwa da mutane a Kano

Binciken jaridar The Nation ya bayyana cewa gwamnoni jam'iyyun PDP da APC sun yi nisa wajen ƙwace akalar jam'iyya.

Gwamnonin sun yi kane-kane sun kan-kane lamurran jam'iyyu, baya ga yin uwa da makarɓiya akan dukkan al'amuran jam'iyyar.

A yayin da wasu masu ruwa da tsaki suka yi nasara akan gwamnonin APC ta hanyar fara takun saka da shugaban kwamitin tsare-tsare na APC, gwamna Mai Mala Buni.

Hakan zai sa gwamnonin PDP su iya takunsu.

Da yawa daga cikin tsaren tsaren gwamnonin zai sake fitowa fili kafin ko kuma lokacin taron ƙasa na jam'iyyar APC a watan Yuni, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.

KARANTA: 2023: Bashir El-Rufa'i ya nuna da yiwuwar mahaifinsa da Tinubu su yiwa APC takara

Kamar yadda bincike ya nuna, wasu jiga jigan gwamnoni suna haɗuwa tare da tattaunawar sirri a Abuja don shirya inda akalar jam'iyya zata dosa a babban zaɓen 2023.

Wasu gwamnonin sun yarda cewa an saɓa yarjejeniyar da aka kulla tun asalin haɗaka; wato majar da akayi a shekarar 2014.

Legit.ng ta rawaito cewa Jam'iyyar PDP ta bukaci wata kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta karbar mata kujerar Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai, tare da gabatar da wasu hujjoji akansa.

Gabanin zaben shekarar 2019 ne Dogara ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Daga baya, Dogara ya sake komawa APC a 2020 bayan ya lashe zaben kujerar wakilcin mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro a majalisar wakilai ta kasa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng