Hotunan tsula-tsulan motocin zamani da Zulum ya mika ga sabon Shehun Borno
- Farfesa Babagana Umar Zulum ya gwangwaje Shehun Borno da sabbin motocin alfarma biyu na zamani
- Ya bai wa Alhaji Abubakar Ibn Garbai motocin ne domin ya samu sauki a yanayin gudanar da mulkinsa
- Basaraken ya nuna jin dadinsa tare da jero addu'o'i da yabo ga Gwamna Zulum a kan kokarin da yake a jihar
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi ya gabatar da motocin alfarma biyu ga sabon Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi domin saukaka masa tafiye-tafiye da al'amuran mulkinsa.
Daya daga cikin motocin akwai kirar SUV Lexus ta 2020 sai wata kirar Toyota Hilux ta 2020.
Babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, Tarfaya Asariya, wanda ya samu rakiyar kwamishinan ayyukan noma, Injiniya Bukar Talba ne suka mika motocin.
KU KARANTA: Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce
Shehun ya cika da murna tare da jero addu'o'in nasara ga Zulum. Ya jinjinawa gwamnan a kan yadda yake mutunta dukkan sarakunan gargajiyan da ke fadin jihar.
KU KARANTA: Koma: Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Najeriya
A wani labari na daban, ministan sufuri Rotimi Amaechi yana fama da gocewar kashi da ya samu, a cikin kwanakin karashen mako aka gano.
A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani, an ga ministan yana yawo da sandar guragu yayin bude wani gidan marayu da makarantar Islamiya a karamar hukumar Kaita ta jihar Katsina.
Duk da har yanzu ba a samu cikakken labarin abinda ya kawo gocewar kashin ba, likitoci sun gano cewa ba babban rauni bane.
Makusancin Amaechi kuma jigo a jam'iyyar APC, Eze Chukwuemeka Eze ya tabbatar da wannan cigaban, jaridar The Nation ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng