Allah ya yi wa Sarkin Kaurun jihar Kaduna rasuwa

Allah ya yi wa Sarkin Kaurun jihar Kaduna rasuwa

- Allah ya yi wa Sarkin Kauru dake jihar Kaduna, Ja'afaru Abubakar, rasuwa a ranar Alhamis sannan an yi jana'izarsa a ranar Juma'a

- Ya mutu yana da shekaru 74 bayan wata gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita yayin da ya bar mata 4 da yara 29

- Mataimakiyar gwamna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta jagoranci zuwa ta'aziya masarautar a ranar Lahadi

Allah ya yi wa mai girma sarkin Kauru na jihar Kaduna rasuwa, Alhaji Ja'afaru Abubakar, sakamakon wata 'yar gajeriyar rashin lafiya da yayi.

Ya rasu yana da shekaru 74 a duniya. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya gaji sarautar ne tun 1993.

Ya rasu a asibitin koyarwa na Barau Dikko dake Kaduna a ranar Alhamis da daddare kuma an birne shi a ranar Juma'a a Kauru.

Allah ya yi wa Sarkin Kaurun jihar Kaduna rasuwa
Allah ya yi wa Sarkin Kaurun jihar Kaduna rasuwa. Hoto daga Isah Halliru Soba
Source: Original

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta jagoranci zuwa ta'aziyya ga mutanen karamar hukumar Kauru da 'yan masarautar Kauru a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Koma: Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Najeriya

Wani dan uwa, kuma abokin marigayin, Mallam Sulaiman Lawal (Jarman Kauru) ya kwatanta sarkin a matsayin mutum mai tsoron Allah da kirki, a cewarsa za a yi kewa.

Ya ce mafarkin marigayin shine ganin cigaban masarautar. Ya mutu ya bar mata 4 da yara 29, Daily Trust ta wallafa.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi ya gabatar da motocin alfarma biyu ga sabon Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi domin saukaka masa tafiye-tafiye da al'amuran mulkinsa.

KU KARANTA: 2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo wa Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a

Daya daga cikin motocin akwai kirar SUV Lexus ta 2020 sai wata kirar Toyota Hilux ta 2020.

Babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, Tarfaya Asariya, wanda ya samu rakiyar kwamishinan ayyukan noma, Injiniya Bukar Talba ne suka mika motocin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel