An samu kwayar cutar korona a 'Ice Cream'

An samu kwayar cutar korona a 'Ice Cream'

- Wani rahoto da hukumar lafiya ta kasar China ta wallafa ya bayyana cewa an samu kwayoyin cutar korona a yankin Tianjin

- Ma'aikatar lafiyar ta ce an siyar da kimanin roba 60 na alewar ga jama'a tare da wasu roba 935 da ake zargin suna shaguna

- An fara samun kwayar cutar korona ne a yankin Wuhan da ke kasar China a shekarar 2019

A cewar wani rahoto daga kafar yaɗa labarai ta ƙasar Sin, an gano samfura uku na alawar ice cream sun gurbata da ƙwayar cutar COVID-19 a yankin Tianjin da ke arewa maso gabashin kasar Sin.

Kimanin kwalaye 4,836 na ice cream ɗin ne wanda kamfanin abinci na Tianjin Daqiaodao ya samar amma aka ce cakuɗe suke da ƙwayar cutar COVID-19, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Yanzu haka an datse robobi 2,089 na alawar ta 'Ice Cream' bayan gano kwayar cutar a cikinsu.

KARANTA: Bidiyo: Murna da farin ciki bayan ran attajirin basarake ya dawo bayan ya kwana daya da mutuwa

Duk da haka, 935 daga cikin akwatuna 2,747 na ice cream ɗin da suka shigo kasuwa an ce suna cikin Tianjin tare da sayar da sama da 60 ga jama'ar da ake tunanin sun dade da lamushe su.

An samu kwayar cutar korona a 'Ice Cream'
An samu kwayar cutar korona a 'Ice Cream' @Thecableng
Asali: Twitter

Binciken farko na annobar cutar ya nuna cewa kamfanin yayi amfani da ɗanyen kayan da suka haɗa da garin madara da aka shigo da shi daga New Zealand da Ukraine wajen samar da alewar wacce ƴan birni ke kauna.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Da yake magana da Sky Sports, Stephen Griffin, masanin ilmin kimiyar ƙwayar cutar Korona wanda ke zaune a Jami'ar Leeds, kasar Ingila, ya bayyana tsoron da hakan zai haifar.

"Da alama wani ne ya kawo kwayar cutar, kuma ba tare da sanin cikakken bayaninsa ba, na fi zargin haka," in ji shi.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da batun bude makarantu sai bayan watan uku.

A cewar kwamitin, bude makarantu a halin yanzu zai kawo babban nakasu ga yaki da annobar korona a karo na biyu.

Shugaban kwamitin, Honarabul Julius Ihonvbere, ya ce gwamnati bata tuntubi majalisa ba kafin sanar da ranar bude makarantu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel