Kotu ta saurari hujjojin da PDP kafa akan karar da ta shigar da Yakubu Dogara

Kotu ta saurari hujjojin da PDP kafa akan karar da ta shigar da Yakubu Dogara

- Wata kotun tarayya da ke birnin tarayya, Abuja, ta fara sauraron karar da PDP ta shigar da Yakubu Dogara

- Gabanin zaben shekarar 2019 ne Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

- Jam'iyyar PDP ta bukaci kotu ta tsige Dogara saboda ya sauya sheka zuwa APC bayan samun nasararsa

Jam'iyyar PDP ta bukaci wata kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta karbar mata kujerar Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai.

Gabanin zaben shekarar 2019 ne Dogara ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Daga baya, Dogara ya sake komawa APC a 2020 bayan ya lashe zaben kujerar wakilcin mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro a majalisar wakilai ta kasa.

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan PDP, Mista Jubril, ya roki kotu ta daga kafa wajen sauraron karar saboda har yanzu Dogara yana sharbar romon zaman mamba a majalisa da tikitin jam'iyyarsu.

KARANTA: Buba Marwa ya karbi ragamar shugabancin NDLEA, ya aika sako ga masu safarar miyagun kwayoyi

Masu Kara; PDP da shugabanta na jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam, sun bukaci Dogara ya bar kujerarsa bisa dogaro da sashe na 68(1) na kundin tsarin mulki, kamar yadda Channels ta rawaito.

A cewarsa, doka ta bukaci dan majalisa ya sauka daga kujerarsa matukar ya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar daban ba tare da jam'iyyarsa na fuskantar wani rikici ba.

Kotu ta saurari hujjojin da PDP kafa akan karar da ta shigar da Yakubu Dogara
Kotu ta saurari hujjojin da PDP kafa akan karar da ta shigar da Yakubu Dogara
Source: UGC

A cewarsu, bai kamata ko kadan Dogara ya cigaba da zama a zauren majalisa da nasarar da ya samu da sunan PDP ba.

Daga cikin wadanda ake kara akwai Yakubu Dogara da kansa, shugaban majalisar wakilai, ministan shari'a, hukumar zabe (INEC) da jam'iyyar APC.

Akuyam ya tabbatarwa da kotu cewa babu wani rikici a jam'iyyar PDP a jihar Bauchi a lokacin da Dogara ya sanar da ficewarsa.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Kazalika, ya bayyana cewa wa'adin Dogara bai kare ba, sannan jam'iyyar PDP ba ta shiga yarjejeniyar hadin gwuiwa da jam'iyyar da Dogara ya koma ba.

Bayan ya sanar da hakan, Akuyam ya ce suna rokon Kotun ta karbe kujerar Dogara sannan ta umarci INEC ta sake gudanar da zabe.

Bayan sauraron lauyan masu Kara da Mai kare Dogara, alkalin kotun, Jastis Okon Abang, ya matso da zama na gaba zuwa rabar 14 ga watan Fabarairu sabanin ranar 5 ga watan Maris.

A wai labarin daban, Legit.ng ta rawaito cewa wasu 'yan bindiga sun kashe wata dattijuwa, Hauwa Umaru, mai shekaru 80 a kauyen Sharu a karamar hukumar Igabi a jihar kaduna.

Kazalika, 'yan bindigar sun kashe jami'an 'yan sanda hudu yayin musayar wuta a hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.

Duk da hakan, IGP Mohammed Adamu ya jinjinawa tawagar 'yan sanda saboda ta dakile harin da 'yan bindigar suka kai musu yayin da suke kan hayarsu ta komawa Kano bayan kammala wani aiki na musamman.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel