An wajabtawa malamai da dalibai saka takunkumi bayan bude BUK
- An sake bude jami'ar BUK tare da shimfida sabbin matakai don kariya daga yaduwar annobar COVID-19
-Jami'ar ta tilasta amfani da takunkumin fuska ga ma'aikata, dalibai da masu kai ziyara makarantar
- Hukumar makarantar ta shawarci ma'abota makarantar da su rage musabaha su kuma bi sauran dokoki don kauracewa hukunci
Hukumar Jami'ar Bayero da ke Kano, BUK, ranar Litinin, ta sanar da wajibcin amfani da takunkumin fuska ga duk ma'aikata, dalibai da masu kai ziyara daga ranar 18 ga Janairu, a matsayin matakin kariya daga yaduwar annobar COVID-19.
Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ya ruwaito cewa an sake bude makarantar ranar Litinin, biyo bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na sake bude makarantu.
Sanarwar ta fito a wata sanarwa da Lamara Garba, sakataren yada labaran jami'ar ya fitar.
DUBA WANNAN: Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa
Malam Garba ya ce an dauki matakin ne saboda kare yaduwar annobar COVID-19 a fadin kasa da kuma taimakawa wajen tabbatar da lafiya ga al'umma.
"Hukumar BUK na sanar da ma'aikata, dalibai da masu kawo ziyara makarantar cewa jami'ar na bin matakan kariya ga annobar COVID-19 a cikin makarantar.
"Saboda haka, ma'aikata (malamai da ba malamai ba), iyalan su da dalibai dama masu kawo ziyara ga jami'ar dole su bi matakan kariyar.
"Tuni, hukumar ta samar da na'urar tsabtace hannu a wuraren da suka dace na dalibai da malamai da ma dakunan kwanan dalibai don amfani da su.
"Babu dalibin da zai shiga aji ko wani waje a cikin jami'ar ba tare da amfani da takunkumin da ya rufe baki da hanci ba.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace matafiya a Omo-Ijesa
"Malamai ma akwai bukatar su sanya takunkumi, su kuma tabbatar duk dalibai sun yi hakan a lokutan karatu.
"Ma'aikata, dalibai da masu ziyara su kasance sanye da tukunkumin tsawon lokacin da suke jami'ar.
"Kuma, wanda ke zaune a jami'ar da masu kai ziyara dole ne ya kasance suna bada tazara yadda ya kamata a wuraren karatu da dakunan kwana da sauran wurare.
"Dole a sanya takunkumi yadda ya kamata, ya zamana ya rufe hanci da baki, kar a sa a kunne daya ko a kasan haba.
"Da cikin matakan kariya da kuma tilasta bin dokar, hukumar jami'ar ta dauki ma'aikatan sa ido tare da jami'an tilasta bin matakan kariyar," a cewar sa.
A cewar sa, duk wanda aka kama yana karya dokar za a dauki mataki a kan sa, yana cewa don a rage yaduwar cutar, dole ma'abota jami'ar su rage yin musabaha, su bada tazara, su kuma wanke hannu akai akai.
A wani labarin daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Kebbi ta ce tana fatan za ta kwace mulki daga All Progressives Congress (APC) a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban jam'iyyar na jihar, Haruna Sa'idu, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da ya ke tarbar jigo a jam'iyyar APC, Abdulmalik Halliru Milton, wadda ya fice daga APC ya koma PDP a Birnin Kebbi.
Sai'idu, ya kuma soki yan majalisar dokokin jihar da ya ce suna bari gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu na juya su duk yadda ya so.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng