'Yan bindiga sun sace matafiya a Omo-Ijesa

'Yan bindiga sun sace matafiya a Omo-Ijesa

- Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu fasinjoji a Omo-Ijesa a jihar Osun

- Rundunar yan sanda da Amotekun sun tabbatar da sace matafiyan sun kuma tura jami'ansu

- Daya daga cikin matafiyan da aka sace ne ya yi nasarar tserewa ya sanar da hukumomin tsaro

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace wasu fasinjoji a Omo-Ijesa da ke karamar hukumar Oriade ta Jihar Osun, Vanguard ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace wasu matafiya a hanyarsu ta dawowa daga wani tafiya.

'Yan bindiga sun sace matafiya a babban titin Ilesa-Akure
'Yan bindiga sun sace matafiya a babban titin Ilesa-Akure. Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za mu kayar da APC a Kebbi, in ji shugaban PDP

Duk da cewa ba a tabbatar da adadi wadanda aka sace ba, wani majiya daga hukumomin tsaro ya shaidawa Vanguard cewa daya daga cikin wadanda aka sace ne kuma ya tsere ya kai wa yan sandan Ijebu-Jesa rahoto.

Kwamandan rundunar Amotekun, Janar Bashir Adewunmi (mai murabus) ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an sace wasu a Omo-Ijesa kuma sun tura jami'ansu don bin sahunsu.

"Da gaske ne an sace wasu mutane a Omo-Ijesa, ba mu san adadinsu ba a yanzu, amma mun aike da jami'anmu domin ceto su," in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22

Kazalika, kakakin yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ita ma ta tabbatar da afkuwar lamarin kuma ya ce sun tura jami'ansu domin ceto wadanda aka sace.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel