Allah kadai zai iya tabbatar da nasarar yaki da rashin tsaro, Adesina

Allah kadai zai iya tabbatar da nasarar yaki da rashin tsaro, Adesina

- Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce ya kamata 'yan Najeriya su fahimci cewa nasara daga Ubangiji kadai take

- A cewarsa, kamar yadda 'yan Najeriya suke yi wa kawunansu addu'o'i kullum, su dinga yi wa sojoji, wadanda suke filin daga addu'o'i

- Adesina ya fadi hakan ne ta wata takarda ta ranar Alhamis, wacce ya tunatar da 'yan Najeriya irin sadaukarwar da sojoji suke yi

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce 'yan Najeriyan da suka ki mika lamurran harkar tsaro a hannun Ubangiji, suna da matsala, kuma su na cigaba da jan yaki akan ta'addanci.

Adesina ya bayyana hakan ne a wata takarda ta ranar Alhamis. Hadimin shugaban kasan ya lura da wani bidiyo wanda ya yi ta yawo na wani soja da wasu mutane 4 suna waka, wacce suke cewa nasara daga Ubangiji kadai take.

Adesina ya ce 'yan Najeriya da dama sun kasa fahimtar cewa nasara daga Ubangiji kadai take, The Punch ta wallafa.

KU KARANTA: Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai

Allah kadai zai iya tabbatar da nasarar yaki da rashin tsaro, Adesina
Allah kadai zai iya tabbatar da nasarar yaki da rashin tsaro, Adesina. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

Kamar yadda ya wallafa, "Ya kamata a ce 'yan Najeriya su gane cewa nasara daga hannun Ubangiji take. Shin muna yi wa rundunoninmu na sojoji masu yaki addu'a? Shin muna tuna matasanmu, ababen alfaharinmu kuma karfinmu, wadanda suke fuskantar mutuwa a kullum?

"Muna yin bacci a gidajenmu, gefen matanmu, amma suna can filayen daga.

"Yayin da muke addu'a kamar Ubangiji ka bani mota, cigaba a wurin aiki, da sauransu, muna tuna sojojinmu kuwa?

"Nasara a wurin Ubangiji kadai take. Idan ba a addu'a, rashin tsaron arewa maso gabas, arewa maso yamma, arewa ta tsakiya da sauran wurare a Najeriya, to tabbas ana kara tsawaita rikicin ne."

Kakakin shugaban kasan ya ce maimakon sukar gwamnati, ya kamata a dinga addu'ar samun nasarori ga gwamnati don kawo karshen tashin hankali.

KU KARANTA: Sojin sama sun yi wa Boko Haram ruwan wuta, sun halaka 'yan ta'adda a Borno

A wani labari na daban, har yanzu, harkokin tsaro sai kara tabarbarewa suke yi, don da safiyar Alhamis, 14 ga watan Janairu wasu mutane, da ake zargin 'yan fashi ne suka kashe wani Mustapha Abubakar a jihar Kano.

Dan uwan Abubakar ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda yace sun harbi dan uwansa ne da safiyar Alhamis.

Kamar yadda yace, Abubakar yana hanyar komawarsa gida daga masallaci mummunan lamarin ya auku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel