Fargabar korona: An bukaci gwamnatin tarayya ta daga bude makarantu sai bayan wata uku

Fargabar korona: An bukaci gwamnatin tarayya ta daga bude makarantu sai bayan wata uku

- Kwamitin majalisar wakilai akan harkar ilimi ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da batun bude makarantu a ranar 18 ga wata

- A cewar kwamitin, bude makarantu a halin yanzu zai kawo babban nakasu ga yaki da annobar korona a karo na biyu

- Shugaban kwamitin, Honarabul Julius Ihonvbere, ya ce gwamnati bata tuntubi majalisa ba kafin sanar da ranar bude makarantu

Majalisa ta nemi Gwamnatin tarayya ta dakatar da batun komawar dalibai Makarantu har zuwa nan da watanni uku masu zuwa.

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da ilimi ya ce batun buɗe makarantu zai iya kawo cikas akan yaƙi da annobar COVID-19.

Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere, ya ce gwamnatin tarayya ba ta tuntuɓi sauran masu ruwa da tsaki kafin ta bada sanarwar komawar dalibai makarantu ba.

Kwanan watan buɗe makarantu na ranar Litinin,18 ga watan Junairu, ya jawo cece-kuce sakamakon ganin baiken shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke, inda suka ce akwai haɗari a bude makarantu saboda Annobar COVID-19.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Da yake maida martani akan buɗe makarantu ranar 18 ga watan Junairu, Honarabul Julius Ihonvbere, shugaban kwamitin majalisa akan ilimi yace buɗe makarantu babbar barazana ce ga yaƙi da annobar COVID-19 a karo na biyu.

Fargabar korona: An bukaci gwamnatin tarayya ta daga bude makarantu sai bayan wata uku
Fargabar korona: An bukaci gwamnatin tarayya ta daga bude makarantu sai bayan wata uku
Asali: Facebook

Ihonvbere ya ce FG bata tuntuɓi majalisa ba kafin yanke shawarar cewa dalibai zasu kara komawa makarantu ranar 18 ga wata ba.

Ya ƙara da cewa a dakatar da komawa makarantun zuwa nan da watanni uku don ganin yadda hali zai yi, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito.

Ya koka akan rashin "daukar mataki ko wani shirin kare ɗalibai daga annobar COVID-19.

"Mun damu ƙwarai akan yawan adadin masu kamuwa da cutar.

KARANTA: Korona: NYSC ta hana taron ibada, ta daga ranar bude sansanin horo

"Duk da kasancewar makarantu a rufe suke, ana samun mutane 500 zuwa 1000, ina kuma ga ace an buɗe makarantu.

"Akan me ake gaggawar buɗe makarantu ba tare da daukar matakan kariya ko wani shiri akan kare rayuwar ƴa'ƴayen mu ba?

"Basu tuntuɓe mu ba, ya kamata aƙalla ace sun tuntuɓi kwamitin mu, ba wanda ya tuntuɓemu koda daga ma'aikatar ilimi ne," a cewar Dan majalisar.

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ce idan har jihar ba ta kasance cikin lumana ba, sauran sassan kasar ba za su taba zama cikin lumana ba.

Sama da shekaru goma, Borno da wasu jihohin arewa maso gabas na fama da hare-hare daga kungiyar Boko Haram, inda aka kashe dubbai tare da raba mutane sama da miliyan biyu da muhallansu.

A lokacin da yake jawabi a wajen taron lakcar shekara ta Gani Fawehinmi karo na 17 a Legas, Zulum ya ce kalubalen tsaro a Borno na da hadari ga kowane bangare na kasar kuma dole ne kowa ya taru ya a yaki hakan.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng