Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe dattijuwa Hauwa Umaru da 'yan sanda hudu
- Wasu 'yan bindiga sun kashe wata dattijuwa, Hauwa Umaru, mai shekaru 80 a kauyen Sharu a karamar hukumar Igabi
- Kazalika, 'yan bindigar sun kashe jami'an 'yan sanda hudu yayin musayar wuta a hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua
- IGP Mohammed Adamu ya jinjinawa wata tawagar 'yan sanda da ta dakile harin da 'yan bindiga suka kai musu
A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa 'yan bindiga sun kashe wata tsohuwa mai shekaru 80 tare da 'yan sanda hudu a wasu hare-hare daban-daban.
Mista Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin jihar Kaduna, shine ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
A cewarsa, 'yan bindigar sun kashe dattijuwar, Hauwa Umaru, mai shekaru 80, yayin harbin kan mai uwa da wabi da suka yi yayin da suka kai hari kauyen Sharu da ke yankin karamar hukumar Igabi.
KARANTA: Bidiyo: Murna da farin ciki bayan ran attajirin basarake ya dawo bayan ya kwana daya da mutuwa
Kazalika, rundunar 'yan sandan Nigeria ta bakin kakakinta na kasa, Frank Mba, ta sanar da cewa ta rasa jami'anta hudu a Kaduna.
Vanguard ta sake rawaito cewa a cikin wata sanarwa da ya fitar, Mba ya ce 'yan sandan sun mutu ne yayin musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.
Kazalika, sanarwar ta kara da cewa IGP Mohammed Adamu ya jinjinawa rundunar 'yan sandan, wacce ke kan hanyar komawa Kano, saboda dakile harin 'yan bindiga a hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.
KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria
A ranar Juma'a, 15 ga wata ne, 'yan bindiga suka kai wa tawagar 'yan sandan hari a hanyarsu ta komawa Kano bayan kammala aiki na musamman a yankin.
Legit.ng ta rawaito cewa wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga sun kai hare tare da kashe mutane takwas a kauyen Janbako da ke yankin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
A cewar Daily Trust, 'yan bindar sun kai hari kauyen akan babura tare da yin harbin kai mai uwa da wabi.
Wani mazaunin kauyen ya tabbatar da cewa 'yan bijilanti sun hallaka wasu daga cikin 'yan bindigar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng