Bidiyo: Murna da farin ciki bayan ran attajirin basarake ya dawo bayan ya kwana daya da mutuwa
- An barke da murna da farin ciki a shafukan sada zumunta bayan wani babban basarake a jihar Imo ya farfado bayan kwana daya da mutuwa
- Basaraken mai suna Ifeanyichukwu Ekeokwu, wanda aka fi sani da Ayiego, ya kwana daya a dakin ajiyar gawa bayan sanar da mutuwarsa
- A ranar 8 ga watan Janairu ne Ayiego ya binne gawar mahaifinsa da ya rasu
Dubban jama'a mazauna jihar Imo sun shiga shafukansu na sada zumunta daban daban suna ikirarin cewa wani babban basarake mai taimakon mutane, Ifeanyichukwu Ekeokwu, wanda aka fi sani da Anyiego na Amiri, ya dawo da rai bayan an bayyana mutuwarsa.
A cewar rahotannin yanar gizo, an riga an ajiye gawar Anyiego a ɗakin ijiye gawarwaki kuma ya yi kwana daya a wurin amma daga baya aka taɓɓatar da farkawarsa.
Haka kuma an ga hoton gawar mai taimakon wacce aka lullube da kyallen rufe gawa yayin da aka dora akan gado na karfe. Wani hoton ya sake nuna gawar mutumin kusa da makara.
Wani mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna, Godwin Chijioke, ya saka wani faifan bidiyo na tashin Anyiego tare da mutanensa suna murna.
Ita ma wata mai suna Ogechi Okoroji ta bayar da da labarin dawowar Anyiego a shafinta na Facebook, inda ta ce; Allah ya cece shi saboda yana da kirki.
Wani shima mai suna, Nnaa Tuu, ya bayyana murna da mamakin dawowar wannan bawan Allah a shafinsa na facebook inda ya ce faruwar hakan ba komai ba ne illa ikon Allah.
Wasu daga cikin wadanda suka yada farfadowar Anyiego sun bayyana cewa a ranar 8 ga watan Janairu ya binne mahaifinsa da ya rasu, lamarin da yasa jama'a da yawa cikin damu bayan sanar da cewa shi ma ya mutu.
Basarake Anyiego ya yi shura wajen taimakon jama'arsa da tallafa musu da kudin aljihunsa, wanda hakan yasa ya zama mai farin jini a wurin mutanensa.
A wani labarin, Legit.ng Hausa rawaito cewa Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram, ƙasashen Turawan Yamma sun fi nuna damuwa da jihar Borno sama da ƙasashen Larabawa waɗanda suma suke fama da irin wannan matsalar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin ambasadan Falasɗinawa, Saleh Fheised Saleh, inda ya jinjinawa yankin na Falasɗinu da zama ɗaya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya.
A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta bawa Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng