Zamfara: 'Yan bindiga sun harbe mutane takwas a Maradun

Zamfara: 'Yan bindiga sun harbe mutane takwas a Maradun

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutane takwas a kauyen Janbako da ke karamar hukumar Maradun

- 'Yan bindigar sun budewa mazauna kauyen wuta bayan dirarsu a kan babura

- Wani mazaunin kauyen ya tabbatar da cewa wasu 'yan bijilanti sun hallaka wasu daga cikin 'yan bindigar

Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hare tare da kashe mutane takwas a kauyen Janbako da ke yankin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

A cewar Daily Trust, 'yan bindar sun kai hari kauyen akan babura tare da yin harbin kai mai uwa da wabi.

"An samu hatsaniya da hargowa a kauyen a yayin da jama'a ke kokarin gudun neman mafaka bayan 'yan bindigar sun dira kauyen tare da budewa wuta.

"Duk da 'yan bijilanti sun mayar da martani tare da kashe wasu daga cikin 'yan ta'addar amma su ma sun kashe mutane takwas yayin da suke gudun neman mafaka domin tsira da rayuwarsu.

KARANTA: Kano: An gano dalilin da yasa kananan yara ke zama 'yan sholisho, an ji ta bakinsu

"Sai da muka bar wasu daga cikin 'yan bijilanti su zama masu gadi domin bawa jama'a kariya yayin da ake jana'izar mutanen da aka kashe.

Zamfara: 'Yan bindiga sun harbe mutane takwas a Maradun
Zamfara: 'Yan bindiga sun harbe mutane takwas a Maradun
Source: Twitter

"Sun kashe mafi yawan mutanen ne yayin da suke kokarin guduwa, maharan sun budewa jama'a wuta.

KARANTA: Bauchi: Ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu ya faskara bayan gobara ta tashi a gidansu

"Muna godiya ga jami'an tsaro da suka kawo mana agajin gaggawa, ba don haka ba barnar da 'yan bindigar zasu yi sai ta fi haka," kamar yadda wani mazaunin kauyen ya shaidawa Daily Trust.

Kokarin Daily Trust na jin ta bakin SP Muhammad Shehu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, bai samu ba har zuwa lokacin wallafa rahoton.

A wani labarin, Legit.ng Hausa rawaito cewa Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram, ƙasashen Turawan Yamma sun fi nuna damuwa da jihar Borno sama da ƙasashen Larabawa waɗanda suma suke fama da irin wannan matsalar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin ambasadan Falasɗinawa, Saleh Fheised Saleh, inda ya jinjinawa yankin na Falasɗinu da zama ɗaya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya.

A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta bawa Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel