Yadda jihohi 27 suka tirsasa gwamnatin tarayya bude makarantu

Yadda jihohi 27 suka tirsasa gwamnatin tarayya bude makarantu

- Jihohi sun tilasta gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a ranar Litinin, 18 ga watan Janairun 2020

- Hakan ya biyo bayan tashin guguwar cutar COVID-19, har PTF ta hana komawa makarantu ranar 18 ga watan Janairu

- Duk da haka jihohi basu tsaya ba, a ranar Talata suka matsa wa minsitan ilimi aka yi taro, don lallai suna son makarantu su koma

Jihohi sun matsa wa gwamnatin tarayya ta amince a koma makarantu ranar Litinin, kamar yadda aka fahimci hakan ranar Alhamis.

Bayan tashin guguwar COVID-19 a karo na biyu, wanda dalilin haka PTF ta sanar da cewa ba za a koma makarantu ba sai ranar 18 ga watan Janairu.

A makon da ya gabata, ministan ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana yana sanar da jama'a cewa babu batun komawa ranar 18 ga watan Janairu, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa

Yadda jihohi 27 suka tirsasa gwamnatin tarayya bude makarantu
Yadda jihohi 27 suka tirsasa gwamnatin tarayya bude makarantu. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Kamar yadda yace, "Za a sake duba ranar da za a koma."

Adamu ya kara da cewa, za a sake canja ranar komawa makarantu, kuma za su duba maganar PTF.

Sai dai, jihohi da dama sun fara azazzala, inda suka fara bude makarantu tun 11 ga watan Janairu, hakan ya janyo ma'aikatar ta gayyaci kwamishinonin ilimi na jihohi 36 zuwa taro a ranar Talata.

Jihohin sun nuna cewa lallai sai sun koma makarantu ranar 18 duk da kokarin ministan wurin janyo ra'ayinsu akan kada su koma.

Lokacin da suka ki amincewa da shawararsa, sai ya kyalesu su yi yadda suka ga dama.

Yanzu haka jihohi 20 sun zabi komawa makarantu ranar Litinin. Jihohi 4 sun ki amincewa, 6 kuma sun ce sun riga sun bude nasu. Sun ce za su bi dokar kariya daga cutar COVID-19.

Daga baya ministan ilimi ya ce za su bi abinda jihohi 33 suka amince, a bude makarantu a ranar Litinin.

KU KARANTA: Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin

A wani labari na daban, rundunar Operation Lafiya Dole a ranar Talata ta ragargaza mayakan ta'addanci na Boko Haram kuma sun lalata motcoin yakin 'yan ta'addan a wani samame da suka kai ta jiragen yaki a Mainok da ke Borno, hedkwatar tsaro tace.

Shugaban fannin yada labarai an tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Enenche ya ce an kai harin ne bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya nuna cewa 'yan bindigan na kai kawo a Jakana-Mainok na jihar da motocin yaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng