Takaitaccen tarihin mutuwar shahadar Ahmadu Bello a Junairun shekarar 1966

Takaitaccen tarihin mutuwar shahadar Ahmadu Bello a Junairun shekarar 1966

Tun a karshen shekarar 1964, wasu tsirarru Sojoji su ka fara kitsa yadda za su kifar da gwamnati. A wancan lokacin jam’iyyar NPC ta su Ahmadu Bello je ta ke da mulki da rinjaye.

Daya daga cikin manyan wadanda su ka fara wannan tunani shi ne Chukwuma Kaduna Nzeogu, wanda a lokacin babban Mai horas da Sojoji ne a makarantar koyon aikin Soja ta Garin Kaduna.

Sai a shekarar 1966 wannan mummunan aiki ya tabbata. Kaduna Nzeogu sun ajiye maganar juyin mulkin a 1964 bayan an dakatar da wani taron Soji da aka shirya za ayi a Kudancin Najeriya.

Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogu ya radawa wannan danyen aiki suna da ‘Operation Damisa’ wanda ya fake da cewa ya na horas da Sojoji ne. An yi irin haka a duk sauran bangarorin kasar.

Manjo T. Onwuatuegwu da kananan Sojoji irin su Laftana A. Azubuogu da Laftana O. Ojukwu, su ne su ka taimakawa Kaduna Nzeogu wajen cin ma burinsa na kashe Firimiyan kasar Arewa.

Tun kafin wannan lokaci an rika nunawa Sardauna za a hallaka shi. A kan hanyarsa ta zuwa Umra a shekarar, Firimiyan ya samu takarda da ta fada masa za a kashe shi, amma bai damu ba.

Bayan ya tafi Saudi domin aikin Umrar sa ta karshe, Sardauna ya kai ziyara kabarin Manzon Allah SAW cikin dare (ganin zai mutu) a kwanan da ya samu ya yi a babban birnin Madina.

Ranar Laraba ne Sardauna da Jama’ansa su ka dawo gida daga Saudi. A wata Ranar Juma’a wanda ta zo daidai da 15 ga Watan Junairun 1966, Kaduna da Dakarunsa, su ka shiga gidan Gamji.

Matashin Sojan ya shiga cikin gidan Firimiyan inda ya rika tambaya har aka nuna masa dakin Ahmadu Bello. Kamar yadda tarihi ya nuna, Sardauna ya fito daga cikin Iyalinsa ya tunkare sa.

KU KARANTA: Meyasa aka kashe Firimiyan Arewa Ahmadu Bello Sardauna?

Takaitaccen tarihin mutuwar shahadar Ahmadu Bello a Junairun shekarar 1966
‘Yan-Tawaye su ka kashe Sardauna wajen juyin mulki
Asali: Facebook

‘Yan tawayen sun yi ta harbe-harbe wanda ya firgita kowa. Wani Mai gadi ya yi yunkurin takawa Jami’in Sojan burki, amma kafin ya iya taba kwari da bakansa, sai ga gawansa zube a kasa.

Cikin tsakar dare, Manjo Kaduna ya yi ido-biyu da Sardaunan Sokoto, wanda Uwargidarsa Hafsat ta yi wuf ta rungume shi ta na kuka, Sojan ya rufe ido ya shiga buda masu wuta har su ka mutu.

Kamar yadda Marigayi Abubakar Gumi ya bayyana a littafinsa, ya iso gidan tsohon Firimiyan ne bayan sallar asuba inda ya iske an yi masa raga-raga da makamai sai hayaki kawai ya ke tashi.

Marigayi Sardaunan Sokoto ya yi wasiyya a biznesa a Garin Wurno kusa da Kakansa Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, amma hakan bai yiwu ba saboda ganin ya yi mutuwar shahada.

Da safiyar 16 ga Watan Junairun ne aka yi wa Sardauna da Mai dakinsa jana’iza, Abubakar Gumi wanda ya na cikin wadanda su ka fi kowa kusanci da Marigayin, ya yi wa’azi a wajen jana’izar.

Bayan nan Chukwuma Kaduna Nzeogu da Dakarunsa sun je gidan rediyo sun sanar da cewa sun kifar da gwamnati, ya kuma kafa dokar ta-baci, wanda wannan ya hana mutane fita ko ina a Gari.

Tun ya na Duniya an fadawa Sardauna cewa ba zai wuce shekarun Kakan sa ba. Firimiyan ya cika ne yayin da ya ke da shekaru 56 ko 57 a Duniya. Bai dai isa 58 da aka taba nuna masa ba.

A karshen rayuwarsa, Ahmadu Bello ya bada karfi wajen aikin addini. Sakamakon haka aka kafa kungiyar JNI, ya kuma dage wajen hada-kan Musulman Duniya, da Musuluntar da Maguzuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel