Sojin sama sun yi wa Boko Haram ruwan wuta, sun halaka 'yan ta'adda a Borno

Sojin sama sun yi wa Boko Haram ruwan wuta, sun halaka 'yan ta'adda a Borno

- Rundunar sojin saman Najeriya ta ragargza 'yan ta'addan Boko Haram a Mainok da ke Borno

- Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa sun halaka 'yan ta'addan masu yawa ta jiragen yaki

- Dakarun sun samu bayanan sirri na wucewar 'yan ta'addan tsakanin Jakana da Mainok

Rundunar Operation Lafiya Dole a ranar Talata ta ragargaza mayakan ta'addanci na Boko Haram kuma sun lalata motcoin yakin 'yan ta'addan a wani samame da suka kai ta jiragen yaki a Mainok da ke Borno, hedkwatar tsaro tace.

Shugaban fannin yada labarai an tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Enenche ya ce an kai harin ne bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya nuna cewa 'yan bindigan na kai kawo a Jakana-Mainok na jihar da motocin yaki.

KU KARANTA: Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina

Sojin sama sun yi wa Boko Haram ruwan wuta, sun halaka 'yan ta'adda a Borno
Sojin sama sun yi wa Boko Haram ruwan wuta, sun halaka 'yan ta'adda a Borno. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Ya ce dakarun sojin saman sun dauka jiragen yaki inda suka fara ragargaza 'yan ta'addan tare da kayayyakinsu.

"Mun kashe 'yan ta'adda masu yawa a yayin samamen," yace.

KU KARANTA: Yahaya Bello: APC ta kusa zama gagarumar jam'iyya da Afrika za ta yi koyi da ita

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Bauchi sun kama wani matashi mai shekaru 19, wanda aka fi sani da Sara-Suka, bisa laifin shirya liyafar lalata da holewa a karamar hukumar Dass dake jihar.

Yayin da 'yan sandan hedkwatar Yan doka dake babban birnin jihar suka fita sintiri a ranar Laraba, kwamishinan 'yan sandan, CP Lawan Tanko Jimeta ya ce wadanda ake zargin sun addabi al'umma da hatsabibanci da kwacen wayoyi.

Ba anan kadai suka tsaya ba, ana zarginsu da shirya wata liyafa, wacce ake zargin ta holewa da lalata ce a garin Dass a ranar 11 ga watan Janairu, The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: