Da duminsa: Allah ya yi wa kwamishinan cikin gida na jihar Sokoto rasuwa

Da duminsa: Allah ya yi wa kwamishinan cikin gida na jihar Sokoto rasuwa

- Allah ya yi wa kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Sokoto rasuwa

- Abdulkadir Jeli Abubakar III ya rasu a ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya

- Ya taba zama kwamishinan yada labarai na jihar kuma darakta a NOA

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Sokoto, Abdulkadirr Jeli Abubakar III ya rasu.

Ya rasu a ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita.

Abubakar kani ne ga Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ya taba rike mukamin kwamishinan yada labarai da kuma darakta a cibiyar wayar da kai ta kasa.

Mamamcin ya rasu ya bar mata biyu da yara masu tarin yawa,

KU KARANTA: Yahaya Bello: APC ta kusa zama gagarumar jam'iyya da Afrika za ta yi koyi da ita

Da duminsa: Allah ya yi wa kwamishinan cikin gida na jihar Sokoto rasuwa
Da duminsa: Allah ya yi wa kwamishinan cikin gida na jihar Sokoto rasuwa. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa

A wani labari na daban, rundunar Operation Lafiya Dole a ranar Talata ta ragargaza mayakan ta'addanci na Boko Haram kuma sun lalata motcoin yakin 'yan ta'addan a wani samame da suka kai ta jiragen yaki a Mainok da ke Borno, hedkwatar tsaro tace.

Shugaban fannin yada labarai an tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Enenche ya ce an kai harin ne bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya nuna cewa 'yan bindigan na kai kawo a Jakana-Mainok na jihar da motocin yaki.

Ya kamata a yi taron 'yan jam'iyyar a ranar 12 ga watan Disamban 2020, amma sai aka daga zuwa mako na biyu na watan Janairun 2021.

Gwamnan jihar Kogi ya ce zai yi aiki tukuru wurin ganin jam'iyyar APC ta samu nasarori a zabukan da za a yi a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: