An kashe 'yan ta'adda 64 cikin mako ɗaya a Yobe, in ji DHQ

An kashe 'yan ta'adda 64 cikin mako ɗaya a Yobe, in ji DHQ

- Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sunyi nasarar kashe yan ta'adda 64 a Jihar Yobe

- Hedkwatar tsaron a ranar Alhamis ta bakin kakakinta, John Enenche ne ta sanar da hakan a Abuja

- Kakakin sojin ya kuma gargadi kan mallakar takin zamani ba bisa ka'ida ba don miyagu na amfani da shi

Hedkwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojoji sun kashe yan ta'addan kungiyar Boko Haram 63 a jihar Yobe cikin mako daya sakamakon gumurzun da suka rika yi da dakarun soji, The Punch ta ruwaito.

A wurin wani taron manema labarai da ta kira a ranar Alhamis a Abuja, Shugaban sashin watsa labarai na rundunar soji, Manji Janar John Enenche ya ce Sojoji da wasu hukumomin tsaro suna cigaba da atisayen da suke yi a sassan kasar.

An kashe 'yan ta'adda 68 cikin mako daya a Yobe, in ji DHQ
An kashe 'yan ta'adda 68 cikin mako daya a Yobe, in ji DHQ. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara

Kakakin sojin ya ce yan ta'addan sun gamu da ajalinsu ne a karamar hukumar Gujba da kauyen Gonan Kaji da ke hanyar Damaturu-Buni Yadi yayin musayar wuta da sojoji.

Ya kuma ce an kwato motocci masu bindiga da bindigu da wasu makamai daga hannun 'yan ta'addan.

Janar Enenche, ya kuma gargadi mutane kan samun takin zamani ba bisa ka'ida ba inda ya yi bayanin cewa amfaninsu kawai wurin noma ne, amma duk da haka akwai miyagu da ke siyansu da mugun nufi.

KU KARANTA: 2023: Matasa za su yi tattaki daga Legas zuwa Bauchi don neman gwamnan arewa ya yi takarar shugaban kasa

A cewarsa, ana iya amfani da takin zamani wurin hada abubuwa masu fashewa ko bam na gargajiya saboda ya kunshi sinadarin ammonium nitrate da ake iya sarrafa shi ya fashe.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Asali: Legit.ng

Online view pixel