Likitan da ya ce ba a taɓa yin shugaba mai 'lafiya' kamar Trump ba ya mutu

Likitan da ya ce ba a taɓa yin shugaba mai 'lafiya' kamar Trump ba ya mutu

- Harold Bornstein, tsohon likitan shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mutu

- Harold Bornstein ya kasance likitan Trump tun daga shekarar 1980 zuwa 2017

- Trump ya raba jiha da tsohon likitansa bayan ya fitar da bayan cewa Trump na shan maganin kara tsawon gashi

Tsohon likitan Donald Trump - da Trump ya yi ikirarin cewa ya fadi a wasika cewa ba za a taba yin shugaban kasa mai lafiyarsa ba ya mutu, kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

Harold Bornstein ya rasu a ranar Juma'a da ta gabata yana da shekaru 73 a duniya a cewar New York Times. Ba a bayyana sanadin rasuwarsa ba.

Likitan da ya ce babu shugaban kasar da ya fi Trump 'lafiya' ya mutu
Likitan da ya ce babu shugaban kasar da ya fi Trump 'lafiya' ya mutu. @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarautar Zazzau: Lauyan Iyan Zazzau ya janye kara

Likitan da ya kware a bangaren yadda jikin dan adam ke sarrafa abinci ya kasance likitan Trump tun shekarar 1980 zuwa 2017.

Bornstein ya yi fice ne a watan Disambar 2015 a lokacin da masu kula da yakin neman zaben Trump suka fitar da wasikar da suka ce shi ya rubuta kan lafiyar Trump.

A cikin wasikar ya ce, "Idan aka zabe Mr Trump, zan iya bada tabbacin babu wani shugaban kasa da aka zaba da ya fi shi lafiya."

Likitan mazaunin New York ya shaidawa CNN a 2018 cewa shugaban kasa ne 'ya fada masa abinda za a rubuta a wasikar' da kansa.

KU KARANTA: 2023: Matasa za su yi tattaki daga Legas zuwa Bauchi don neman gwamnan arewa ya yi takarar shugaban kasa

"Ba ni na rubuta wasikar ba. Kawai na yi abinda ya ce ne," in ji Bornstein.

Bornstein na fatan cigaba da kasancewa likitan Trump bayan ya shiga White House amma hakan ba ta yi wu ba bayan ya shaidawa New York Times cewa shugaban kasar na shan magani don kara tsawon gashin kansa.

Bornstein ya shaidawa NBC News cewa bayan labarin ya fito a jaridar Times, wasu masu tsaro ya afka ofishinsa da ke Park Avenue ya kwashe dukkan bayanan lafiyar Trump.

A wani labarin daban, lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: