Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7

Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7

- A ranar Juma'a yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Maru a jihar Zamfara

- Yan bindigan sun yi awon gaba da mutane 7 duk yan gida daya

- Shugaban jam'iyyar APC na garin yace 'yayansa ne duka aka sace

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC a karamar hukumar Maru na jihar Zamfara, Alhaji Sani Gyare, ya bayyana cewa sai bayan awanni da suka kira yan sanda suka zo yayinda yan bindiga suka kai hari yankinsa ranar Juma'a.

Gyare, wanda an bindiga sukayi awon gaba da yaransa bakwai a ranar Juma'a, ya bayyana bacin ransa ga jami'an tsaro, inda yace dukkan shugabanni su ji tsoron Allah wajen aiwatar da ayyukansu.

Yayin magana da jaridar Punch, Sani Gyare ya ce yan bindigan sun dauke yaransa ne saboda rashin jami'an tsaro.

"Yayinda yan bindigan suka shiga kauyen, an sanar da yan sanda, amma basu zo ba sai bayan awanni uku da yan bindigan suka tafi," yace.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya su kawo masa dauki su ceto yaransa.

Hakazalika ya yi kira da jama'a su taimaka masa da addu'a Allah ya bayyana yaransa.

A cewarsa, yaransa da aka sace sune Bashar, Abubakar, Haruna, Habibah, Sufyanu, Mubarak da Armiyau.

Gyare ya ce har yanzu yan bindigan basu kirasu don bayyana bukatunsu ba

KU KARANTA: Kwana 3 jere, sama da sabbin mutane 1500 suka kamu da Koronan kullum

Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7
Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7
Asali: Twitter

KU DUBA: Kwamishanar lafiyan jihar Kaduna ta kamu da cutar Korona

A bangare guda, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa za'a kawo karshen ta'addancin da barandanci wannan shekarar ta 2021, a cewar rahoton The Nation.

Ya yi kira ga al'umma su taimakawa sojoji da addu'a domin taimaka musu wajen kawo karshen rikicin.

Shugaban kasa, wanda ya samu wakilcin Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi, a addu'ar ranar tunawa da Sojojin Najeriya da akayi a babban Masallacin tarayya dake Abuja, ya bada tabbacin cewa "wannan shekaran zamu kawo karshen abinda mukeyi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel