Rahama Sadau na fuskantar caccaka sakamakon hoton da ta saki a yanar gizo

Rahama Sadau na fuskantar caccaka sakamakon hoton da ta saki a yanar gizo

- Jarumar Kannywood, Rahama sadau, na fuskantar caccaka daga masoyanta Musulumai sakamakon bayyana bangaren jikinta

- Mabiyan jarumar sun mayar mata da martani kan hoton da ta ɗauka da jarumar masana'antar Bollywood, Shabnam Surayyo

- Sai dai jarumar ta dawo shafinta na Tuwita ta wallafa wata maganar da Priyanka Chopra ta taba yi akan jajiracewa yayin suka da tsangwama

A kwanakin baya ne jarumar masana'antar Kannywood, Rahama Sadau, ta sha ragargaza a shafukan sada zumunta sakamakon saka wata sutura da ta bayyana wani bangaren jikinta a fili ƙarara.

A yanzu haka Jarumar tana ƙara shan caccaka daga masu bibiyarta Musulmai a shafukan sada zumunta na zamani.

Wasu hotuna da ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta ya harzuƙa wasu Musulmai masu bibiyarta har sun mayar mata da zafafan raddi a ɓangaren maida martani.

Masu bibiyarta Musulmai sun ce ta bayyana sashin ƙafaɗarta wanda ya saɓawa koyarwa da tarbiyar addinin Islama da Hausawa.

KARANTA: FG ta rattaba hannu kan kwangilar gina layin jirgin kasa daga Kano - Maradi da Kano - Dutse

Ɗaya daga cikin mabiyanta ya yi kira ga jarumar da ta daina amfani da sutturar turawa maimakon haka ta tallata sutturar Arewacin Najeriya.

Rahama Sadau na fuskantar caccaka sakamakon hoton da ta saki a yanar gizo
Rahama Sadau na fuskantar caccaka sakamakon hoton da ta saki a yanar gizo
Asali: Instagram

"Ba kwaikwayon su ya kamata kiyi ba don burgesu, kina da ikon tallata nau'in sutturarmu ta Arewacin Najeriya a duniya @Rahma_Sadau.

"Za ki iya nunawa duniya irin kyawu da ƙwarewar mu a fannin kayayyaki da suturar Arewacin Najeriya.....Ba ma buƙatar kwaikwayon su ."

KARANTA: Ahmed Musa ya sha nasiha da shawarwari bayan ya yada wani hotonsa da matarsa a dandalin sada zumunta

Hakama wani daga cikin mabiyanta ya ce suttura da ta sa ba irin sutturar da duk mai neman albarkar Allah zai sanya jikinsa bane tare da shawartar Jarumar da ta rufe gashin kanta.

Ku kalli abin da jarumar ta wallafa.

"A cikin shirin film ɗin Star's Defence,wani ɗan uwa musulmi ya yi kira ga mutane kan su daina yankewa jarumar hukunci."

Awanni kaɗan bayan ta wallafa hoton, jarumar ta ɗauko maganar Jarumar Bollywood, Priyanka Chopra, inda take magana akan jajiracewa yayin fuskantar suka da tsangwama.

A makonnin da suka gabata ne Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda aka tilasta jarumar bawa al'ummar Musulmi haƙuri sakamakon ɓatanci da hotunan suka haddasa akan Annabi SAW.

Jarumar tayi alƙawarin hakan ba zata sake faruwa ba. Har ma ta fashe da kuka lokacin da take roƙon gafara daga masoyanta musulmai.

A baya Legit.ng ta rawaito cew Rahama Sadau ta gana da kwamishinan fina-finai na Quebec, kasar Canada amma a Dubai.

Jarumar ta sanar da hakan a wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram tare da hotonsu.

Ta sanar da cewa suna tattaunawa a kan yuwuwar fim din hadin guiwa tare da su.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel