Faifan bidiyon sabuwar wakar Hausa ya fusata Hausawa a dandalin sada zumunta
- Al'ummar Hausawa ma'abota amfani da dandalin sada zumunta sun yi Alla-wadai da tofin Ala-tsine akan sakin wani faifan sabuwar wakar Hausa
- Wani mawaki ne mai suna Abdullahi Aliyu Shelleng, haifaffen jihar Adamawa, ya rewa wakar mai suna 'North Vibe'
- Wasu daga cikin masu sukar wakar sun nemi a goge faifan bidiyon daga yanar gizo sannan dauki hukuma ta dauki mataki
Sakin wani faifan bidiyon sabuwar wakar Hausa a shafin YouTube da sauran dandalin sada zumunta ya fusata Hausawa tare da yin tofi Alla-wadai da da wakar, wacce suka ce ta sabawa al'ada Bahaushe.
Wadanda suka soki sabuwar wakar, mai suna 'North Vibe' wacce mawaki Abdullahi Aliyu Shelleng ya rera kuma ya wallafa, sun yi korafin cewa an nuna tsiraici a faifan bidiyon wakar.
Jaridr Daily Trust ta rawaito cewa mawakin, wanda aka fi sani da AA Shelleng, haifaffen jihar Adamawa ne kuma ya nadi faifan bidiyon sabuwar wakar tare da wani mawaki mazaunin Legas mai suna SlimCase.
KARANTA: Ahmed Musa ya sha nasiha da shawarwari bayan ya yada wani hotonsa da matarsa a dandalin sada zumunta
Sabuwar wakar ta fusata Hausawa a dandalin sada zumunta lamarin da yasa suka yi rubdugun wajen yin martani tare da zargin cewa faifan bidiyon wakar ya ci mutuncin yare da al'adun Hausa.
Wani mai suna Tajuddeen Musbahu ya mayar da martani kamar haka; "wannan ya sabawa al'adu da tarbiyar arewa. Wannan tamkar cin mutunci ne ga duk mutanen da ke yaren Hausa, ina mai bayar da shawarar a goge wannan faifan bidiyo daga yanar gizo domin bai kamata ba, kuskure ne."
KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta karrama marigayi AIG Bishi da faretin bankwana, an binne gawarsa cikin hawaye
Wani mutum ya sake bayyana nasa ra'ayin kamar haka; "na tabbata wannan gayen ba dan arewa bane, babu yadda za'a yi Bahaushe ya yi haka ba tare da an samu mai tsawatar masa ba. A takaice, babu wata kabila a Nigeria da zata so a alakanta ta da wannan faifan bidiyo.
"Ya kamata hukuma ta dauki mataki a kan wannan yunkuri na son cin mutunci da zubar da kimar wani yare ba tare da wani dalili ba.
A ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, Legit.ng ta rawaito cewa Jarumar Kannywood, Rahama sadau, na fuskantar sabuwar caccaka daga masoyanta Musulumai sakamakon bayyana bangaren jikinta
Mabiyan jarumar sun mayar mata da martani kan hoton da ta ɗauka da jarumar masana'antar Bollywood, Shabnam Surayyo
Sai dai jarumar ta dawo shafinta na Tuwita ta wallafa wata maganar da Priyanka Chopra ta taba yi akan jajiracewa yayin suka da tsangwama.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng