Magabatanmu basu fuskanci haka ba, Matashi ya koka a kan hidimar aure

Magabatanmu basu fuskanci haka ba, Matashi ya koka a kan hidimar aure

- Matashi daga yankin kudancin kasar nan ya koka da tsawwalawar da ake yi a kan aure

- Ya ce dole ne matasa su hada kai wurin kokarin ganin an sassauta yayin da suke neman aure

- Yin korafinsa ke da wuya a Twitter matasa suka dinga goyan bayansa tare da sukar al'adu

Wani mutumi daga yankin arewa maso gabas na kasar nan ya kalubalanci yadda ake tsawwala al'amuran aure a kasar Ibo.

A yayin da ya yi dogaro da wani lissafi tare da jerin kayan da ake bukata ango ya kaiwa dangin amarya a Nnewi na jihar Anambra, mutumin ya yi korafin ta shafinsa na Twitter.

Ya ce matasa a kasar Ibo suna shan wahala. Ya dace a rage yawan abubuwan da ake bukatar matashi ya kai idan yana neman aure.

KU KARANTA: Femi Fani-Kayode ya samu karuwa, budurwarsa ta sunkuto masa yaro namiji

Magabatanmu basu fuskanci haka ba, Matashi ya koka a kan hidimar aure
Magabatanmu basu fuskanci haka ba, Matashi ya koka a kan hidimar aure. Hoto daga @Kene_Nnewi
Asali: Twitter

Ya wallafa: "Na yi watsi da wannan lamarin a Umunna kuma zan yake shi iyakacin iyawata. Idan za ka iya, ka yi yaki da na yankinka.

"A kodayaushe aure a kasar Ibo tsada yake karawa. Na sanar da mutane ne cewa dole a rage yawan lemun da ake kaiwa ko kuma a hakura da su.

"A karba N70,000 na akuyoyi biyu, N10,000 na lemo shikenan. Dole ne a rage taron da ake yi ana shan kwalba 8 kowanne mutum daya."

Wani ma'abocin amfani da Twitter kuwa martani yayi da cewa, "Al'adar Africa kullum kara wahala take."

Kene ya ce ba haka bane, mugunta ce da zari wanda magabatanmu basu taba yin irin shi ba.

"Ba al'adar Afrika bace illa mugunta da zari wanda magabatanmu basu taba yin irin shi ba."

KU KARANTA: Da duminsa: An tsinci gawar daraktan ma'aikatar noma a cikin ofishinsa

A wani labari na daban, Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, ya ce shugaban kasa bai sallami shugabannin tsaro ba ne saboda yana hango wata nagartarsu da 'yan Najeriya basu gani.

Shehu ya sanar da hakan a wani bakuncinsa da TVC ta karba kuma jaridar Vanguard ta ruwaito.

A yayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan abinda ya hana Buhari ya sallami shugabannin tsaro duk da yadda ake ta bukatar yayi hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel