Tsohon Kakakin Jihar Kaduna, Jumare, ya rasu

Tsohon Kakakin Jihar Kaduna, Jumare, ya rasu

- Tsohon dan majalisar dokokin Jihar Kaduna Abdullahi Jumare ya rasu bayan fama da gajeriyar jinya

- Marigayin ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin Kaduna daga shekarar 2012-2015

- An yi jana'izar sa a karamar hukumar Makarfi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar

Daya daga cikin tsofaffin kakakin majalisar Jihar Kaduna, Ahmed Hassan Jumare ya rasu. Jumare ya mutu bayan gajeriyar jinya da daren ranar Talata. Shine kakakin majalisar daga 2012 zuw 2015.

Tsohon kakaki kuma dan majalisa mai ci, Dr Aminu Shagali ne ya tabbatar da labarin a shafin sa na Twitter, ya na cewa, "muna bakin cikin sanar da rasuwar tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna daga shekarar (2013-2015) Hon. Ahmad Hassan Jumare (Branco), wanda ya rasu bayan gajeriyar jinya, Allah ya yafe masa kurakuren sa ya kuma bashi aljanna."

Marigayin, tsohon mai bawa mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo shawara ne kan al'amuran siyasa, kuma shi ne mataimakin shugaban jamiyyar PDP a Jihar Kaduna kafin rasuwar sa, The Punch ta ruwaito.

Tsohon Kakakin Jihar Kaduna, Jumare, ya rasu
Tsohon Kakakin Jihar Kaduna, Jumare, ya rasu. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mai garkuwa ya biya N1.5m don fansar kansa daga hannun 'yan bindiga da suka sace shi

Da take nuna alhini, jamiyyar PDP a jihar ta bayyana dan majalisar a matsayin mutumin kirki kuma abokin tafiya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ta ya fitar, Abraham Alberah Catoh ya ce, "Reshen jamiyya na Jihar Kaduna na bakin cikin sanar da rasuwar daya daga cikin manyan shugabannin ta, Rt. Hon. Ahmed Jumare (Branco).

"Ya taba rike mukamin shugaban majalisar zartarwa a karamar hukumar Makarfi, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban jamiyyar PDP a jihar.

KU KARANTA: Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da 'yan bindiga a Katsina

"Mutumim kirki ne kwarai da gaske, abokin tafiya kuma kwararren dan siyasa wanda yayi gwagwarmaya wajen samar da al'umma na gari.

"Zamu yi kewar shawarwari da mutuntaka irin taka."

Tuni aka binne Jumare kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a karamar hukumar Makarfi.

A wani labari na daban, wata budurwa yar kasar kamaru da ke karatun zama ma'aikaciyar jinya, Petra Nji ta rasu a hatsarin mota kwanaki biyar kafin a daura mata aure.

Petra da mijin da za ta aura, Isbias Forsack suna hanyarsu ta dawowa daga Douala ne bayan zuwa daukan hotunan kafin aurensu inda hatsarin ya ritsa da su a kan titin Tiko-Douala a ranar Litinin, 11 ga watan Janairun 2021.

Isbias da sauran fasinjojin da ke cikin motar sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su zuwa wani asbiti da ke kusa amma ita Petra ta mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel