Mai garkuwa ya biya N1.5m don fansar kansa daga hannun 'yan bindiga da suka sace shi
- Mai garkuwa ya biya dan uwan sa mai garkuwa fansar miliyan daya da rabi bayan da ya fada komar sa
- Amodu shi ne wanda Buba ya yi garkuwa da shi, ya bayyana cewa Buba na da alaka da Boko Haram
- Buba ya ce dalilin da ya sa ya ce rashin adalci wajen raba kudin fansa ya sanya shi kafa ta sa kungiyar bayan ya balle daga wajen uban gidansa
Wani dan garkuwa da aka sani da Mohamed Amodu, ya ce sai da ya biya N1,555,000 don ya fanshi kansa daga hannun wani dan garkuwar, Buba Babu dan shekara 35.
Jami'in hulda da jama'a, CP Frank Mba, wanda yayi farautar gaba daya da yan garkuwar a ranar Litinin, ya ce Babu dan garkuwa ne da ya shahara a Abuja da kewaye, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Mba ya kara da cewa Babu ya shahara wajen garkuwa da mutane a manyan titunan Abuja.
DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa
Ya ce, Babu shi ne jagora na uku na tawagar yan garkuwa da wani Buji ke jagoranta, wanda yan sanda su ka kashe shi da mataimakin sa.
Mba ya ce Babu ya ci gaba da jan ragamar tawagar kuma ya shahara wajen kashe wanda yayi garkuwa da su.
Babu ya dauke Amodu zuwa ikon sa kuma da ya yi gardamar biya, an harbe shi a hannu.
Mba ya ce Mohamed ne yayi ikirarin cewa ya na da asiri kuma ko an harbe shi bazai yi masa komai ba sai Babu ya harbe shi don ya tabbatar da abin da ya fada.
Mai magana da yawun yan sandan ya ce Babu na da alaka da babbar kungiyar ta'addanci a arewacin Najeriya.
Mba ya bayyana Amodu a matsayin sannanne wanda ake girmamawa a duniyar ta'addanci.
"Amma an yi garkuwa da shi kuma sai da ya biya miliyan daya da rabi kafin a sake shi," inji Mba.
Amodu, wanda ke da hannu a cikin wasu ayyukan garkuwa fiye da yadda zai iya tunawa, ya bayyana cewa anyi garkuwa da shi ne bayan ya kai wa Babu harsashi guda 90.
Amodu ya ce Buba na da alaka da Boko Haram, kuma sai da yabiya kudin fansa sannan ya kubuta.
Amodu ya ce akwai lokacin da tawagar sa ta yi garkuwa da mutane 20 a lokaci guda.
DUBA WANNAN: Abinda yasa aka canja ni a 'Kwana Casa'in', Safiyya
Ya ce ya tara har miliyan 15 ta hanyar bakar harkallar tasa.
Ya ce ya taba ganin lokacin da Buba ya yi garkuwa da mutane 55 cikin wata mota kirar "luxurious" a lokaci daya.
Da yake magana, Buba ya ce shekarar sa uku ya na garkuwa da mutane.
Ya ce a matsayin sa na shugaba ya na tura yaran sa manyan tituna don yi masa aiki kuma baya shiga cikin gari.
Ya ce ya balle daga kungiyar Buji don kafa ta sa saboda rashin adalci wajen raba kudin fansa.
A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.
A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.
Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng