Ahmed Musa ya sha nasiha da shawarwari bayan ya yada wani hotonsa da matarsa a dandalin sada zumunta
- Wasu mabiyan dan wasan kwallon kafa ta kungiyar Super Eagles, Ahmed Musa, sun nemi ya cire hotonsa da ya saka tare da matarsa
- Ahmed Musa ya saka hotonsa tare da matarsa ta na sumbatar kuncinsa cikin farinciki da annashuwa
- Sai dai, wasu mabiyansa sun ce hakan ya ci karo tare da sabawa tarbiyar addinin Musulunci
Kwararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa, Ahmed Musa, ya sha suka tare da nasihohi da bayar da shawara a kan yada hotunansa tare da matarsa a dandalin sada zumunta.
A hoton, za'a iya ganin Ahmed Musa cikin farinciki da annashuwa yayin da matarsa ke sumbatarsa a kunci.
Sai dai, bayan dan wasan ya saka hoton a shafinsa na sada zumunta, wasu mabiyansa sun nuna rashin jin dadinsu tare da neman ya cire hoton saboda, a cewarsu, ya sabawa tarbiyar addinin Musulunci.
Ahmed Musa ya yada hoton ne a Shafinsa na Facebook domin nuna farinciki da jin dadin kasancewa tare da matarsa da 'ya'ya.
Ga yadda wasu mabiyansa suka mayar martanta akan hoton:
KARANTA: PDP ba ta da sauran wani tasiri a Nigeria; Tsohon gwamnan jam'iyyar daga arewa ya tsallaka APC
Wasu daga cikin raddi akan hoton sun bayyana cewa dan wasan ya fi karfin irin wannan halayya ta wasu daidaikun gamarin mutane na yada hotunansu tare da iyalinsu a dandalin sada zumunta.
Sai dai, Ahmed Musa bai tankawa masu raddin ba, kazalika bai cire hotunan ba kamar yadda suka bukata.
A ranar Litinin ne Legit.ng ta rawaito cewa Hukumar kula da lafiya a matakin farko (NPHCD) ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta fitar da jadawalin rabon alluran rigakafin korona ga jihohi.
Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) ta ce za'a duba alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar korona a jihohi wajen rabon alluran rigakafin.
An samu adadin sabbin mutane 1,585 da suka sake kamuwa da kwayar cutar korona a Nigeria a ranar 9 ga watan Janairu.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng