Rundunar 'yan sanda ta yi wa marigayi AIG Bishi faretin bankwana, an binne gawarsa a Legas

Rundunar 'yan sanda ta yi wa marigayi AIG Bishi faretin bankwana, an binne gawarsa a Legas

- Babban jami'in dan sanda, Omololu Bishi, mai mukamin AIG ya yi mutuwar bazata bayan kara masa girma

- A ranar 18 ga watan Disamba, 2020, IGP Mohammed Adamu ya karawa marigayi AIG Bishi mukami zuwa AIG mai kula da makaman rundunar 'yan sanda

- Rundunar 'yan sanda a karkashin jagorancin AIG Ahmed lliyasu ta gudanar da faretin ban kwana da AIG Bishi

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gudanar da fareti mai kayatarwa domin bankwana da marigayi AIG Omololu Bishi, wanda aka binne gawarsa a Legas.

Marigayi Bishi, mai mukamin mataimakin Sufetan Ƴansandan Najeriya mai kula da makaman rundunar ƴan sanda a hedikwatar ta da ke Abuja, an binne shi a maƙabartar Ebony Vaults da ke Ikoyi.

AIG Bishi ya rasu ne ranar Litinin a wani asibiti da ke Ikeja, Legas, inda aka kwantar da shi bayan ya kamu da rashin lafiyar da ba'a bayyana ba.

Biyo bayan rasuwarsa ne babban sifeton rundunr 'yan sanda, IGP Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin a yi masa jana'izar karramawa ta musamman, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

AIG na Zone 2, AIG Ahmed Iliyasu, shine ya jagoranci jami'an ƴan sanda a Lagos don wakiltar Babban Sufetan ƴan sanda, IGP Abubakar Adamu, wajen ƙaddamar da fareti don karrama Marigayin, babban Jami'in Rundunar.

KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga fiye da 10 da soja daya sun mutu yayin kazamin musayar wuta

Marigayin wanda ya tashi a tsibirin Legas (Lagos Island) ya samu ƙarin matsayi zuwa muƙamin mataimakin babban sifeta (AIG) a ranar 18 ga watan Disamba, 2020.

An ɗauke shi aiki a rundunar ƴansanda a shekarar 1988 a matsayin ƙaramin mataimakin Sufiritandan ƴansanda.

Rundunar 'yan sanda ta yi wa marigayi AIG Bishi faretin bankwana, an binne gawarsa a Legas
Rundunar 'yan sanda ta yi wa marigayi AIG Bishi faretin bankwana, an binne gawarsa a Legas
Asali: Twitter

Rundunar 'yan sanda ta yi wa marigayi AIG Bishi faretin bankwana, an binne gawarsa a Legas
Rundunar 'yan sanda ta yi wa marigayi AIG Bishi faretin bankwana, an binne gawarsa a Legas @Premiumtimesng
Asali: Twitter

Ya rasu ya bar mata da ƴa'ƴa.

AIG Ahmed Iliyasu, wanda ya jagoranci farenti karrama gawar marigayin, ya samu rakiyar Kwamishinan ƴan sandan Jihar, CP Hakeem Odumosu, Kwamandojin yanki,Ƴansandan kwantar da tarzoma da sauran manyan jami'an ƴansanda.

KARANTA: Alhaji Ahmed, tsohon dan takarar gwamna, jigo a PDP ya rasu

Jana'izar tasa ta samu halartar iyalansa, wakilan Sarkin Legas (Oba of Lagos), abokan aikinsa, ƴan uwa da sauran abokan arziƙi.

AIG Ahmed Iliyasu ya nuna kaɗuwarsa da mutuwar bazatar AIG Omololu Bishi,wanda ba'a daɗe da ƙara masa matsayi zuwa muƙamin AIG ba.

Ya bayyana jami'in a matsayin jajurtacce, mai ƙwazo, da aiki tuƙuru.

Ya yi ta'aziyya da jaje ga iyalan mamacin, Sarkin Lagos da abokansa bisa rasuwar Marigayi Bishi.

Ya yi addu'ar Allah ya basu haƙurin juriyar wannan rashin.

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattijai, ya ce bai zama shugaban majalisar dattijai a shekarar 2015 ba saboda ba'a lokacin Allah ya tsara zai hau kujerar ba.

Sanata Lawan ya bayyana hakan ne yayin wani taron ta ya shi murnar cika shekaru 62 da aka shirya a Abuja.

Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai, Lawan ya ce duk da bai samu nasara a wancan lokacin ba, hakan bai hana shi yin aiki hannu da hannu da Bukola Saraki ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel