Hotunan tsuleliyar budurwa da ta zama likita sun gigita samari, suna mika kokon bararsu

Hotunan tsuleliyar budurwa da ta zama likita sun gigita samari, suna mika kokon bararsu

- Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Bello Mariam ta wallafa kyawawan hotunanta yayin da ta zama likita

- Tuni hotunan Mariam suka bazu a kafafen sada zumunta inda mutane ke ta wasa kyanta da iya saka kayanta

- Samari ba su kakkauta ba suka dinga mika kokon bararsu tare da bukatar aurenta saboda babbar martabar da ta samu

Budurwa 'yan Najeriya mai suna Bello Mariam ta zama abun magana a kafar sada zumuntar zamani na Twitter bayan da ta zama cikakkiyar likita.

A wata wallafa da tayi a ranar Juma'a 8 ga watan Janairun 2021, budurwar ta sanar da cewa ta dauka rantsuwarta ta na zama likita kuma tana farin ciki.

Samari da yawa sun tafi shashin tsokaci domin mika kokon barar soyayyarsu gareta.

Domin murnar, Mariam ta wallafa kyawawan hotunanta hutunanta hudu sanye da kaya daban-daban, lamarin da ya kara gigita samari.

Hotunan tsuleliyar budurwa da ta zama likita sun gigita samari, suna mika kokon bararsu
Hotunan tsuleliyar budurwa da ta zama likita sun gigita samari, suna mika kokon bararsu. Hoto daga @mo_dupsie
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)

A yayin rubuta wannan rahoton, wallafarta ta samu jinjinar mutane 12,000. Legit.ng ta tattaro tsokacin jama'a kamar haka:

Wani mai amfani da @EniDaYungBoSS cewa yayi: "Wannan ai jakar kudi ce. Ka aureta ku kama hanya zuwa Amurka ko Canada."

@malikfawas kuwa cewa yayi, "Ina taya ki murna! Amma kada ki ce a Najeriya za ki yi aiki."

A wani labari na daban, wani mutum dan Najeriya ya bayyana yadda rayuwar aurensa na shekaru 7 ta kasance tsakanin matarsa da mahaifiyarsa wacce bata kaunarta ko kadan, a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Mutumin ya ce dama can mahaifiyarsa bata son matar da ya aura. Bai sanar da dalilanta na hakan ba, amma ya bayyana yadda ya amince da kaddararsa, ya cigaba da zama da matarsa na shekaru 7.

Kamar yadda ya wallafa, "Shekaru 7 kenan ina zaune da matata, amma mahaifiyata bata son ta. Tuni na amince da kaddarata na cigaba da rayuwa a haka."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel