Da duminsa: Cutar korona ta kashe wani fitaccen dan Najeriya

Da duminsa: Cutar korona ta kashe wani fitaccen dan Najeriya

- Mutanen jihar Edo sun tashi da alhinin mutuwar dan su, tsohon kwamishina a jihar, Didi Adodo

- Ya rasu ne da safiyar Talata, 12 ga watan Janairu bayan fama da cutar COVID-19 na kwanaki

- Adodo ya rike kujerar kwamishinan kwadago da ayyuka na musamman lokacin mulkin Adams Oshiomhole

The Nation ta ruwaito yadda Kwamared Didi Adodo, tsohon kwamishinan kwadago da ayyuka na musamman na jihar Edo ya rasu.

Shugaban kwadagon ya mutu ne da safiyar Talata, 12 ga watan Janairu, bayan fama da cutar COVID-19 na tsawon kwanaki.

Tsohon kwamishinan ya rike kujerar sakataren ISSSAN kafin rasuwarsa.

Adodo dan Iruekpen ne, karamar hukumar Esan ta yamma dake jihar, kuma ya rike kujerar kwamishina na tsawon shekaru 8, lokacin mulkin Adams Oshiomhole.

KU KARANTA: Aljannar duniya: Bidiyon katafaren gidan Floyd Mayweather mai darajar N3.8bn

Da duminsa: Cutar korona ta kashe wani fitaccen dan Najeriya
Da duminsa: Cutar korona ta kashe wani fitaccen dan Najeriya. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Tun bayan bullowar cutar korona a Najeriya a farkon shekarar da ta gabata, cutar tana cigaba da lamushe rayukan jama'a.

Ta fara lafawa a kwanakin baya amma cikin kwanakin nan mugunyar cutar tana cigaba da hauhawa.

KU KARANTA: 'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)

A wani labari na daban, an shiga cikin tashin hankali da rudani da safiyar Litinin a ma'aikatar noma da habaka karkara dake kan titin Jabba a Iloron, lokacin da aka tsinci gawar wani darekta, Dr Khalid Ibrahim Ndaman a ofishinsa.

Vanguard ta tattaro bayanai akan yadda Dr Ndaman ne darekta na bangaren dabbobi a ma'aikatar har zuwa mutuwarsa, inda aka ga gawarsa da safiyar ranar.

An gano cewa daya daga cikin ma'aikatan ya je ofishin domin su tattauna dashi akan wani al'amari na ma'aikatar, a nan ne ya gan shi a mace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel