Katsina: An yi kazamar musayar wuta, 'yan bindiga fiye da 10 da soja daya sun rasu

Katsina: An yi kazamar musayar wuta, 'yan bindiga fiye da 10 da soja daya sun rasu

- An yi musayar wuta tsakanin 'yan bindiga da dakarun rundunar soji a kananan hukumomin jihar Katsina guda biyu

- A yayin dukkan musayar wutar, dakarun rundunar soji sun kashe 'yan bindiga biyar

- A cewar Birgediya Janar Benard Onyeuko, rundunar soji ta kam wasu mutane uku da ke taimakon 'yan bindiga da bayanan sirri

A ranar Talata ne rundunar soji ta sanar da cewa ta hallaka a kalla 'yan bindiga goma tare da raunata wasu masu yawa yayin wani kazamin musayar wuta da 'yan ta'addar a kananan hukumomin Batsari da Faskari a jihar Katsina.

Kazalika, rundunar sojin ta bayyana cewa ta yi rashin jami'inta guda daya yayin da wasu biyu suka samu raunuka yayin musayar wutar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Da ya ke sanar da hakan cikin wani jawabi da aka rabawa manema labarai a ranar Talata, mukaddashin darektan yada labarai a rundunar soji, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya ce sojoji sun kama mutane uku da ke taimakon 'yan bindigar.

Kazalika, Onyeuko ya sanar da cewa dakaru soji sun samu nasarar kwace makami masu dumbin yawa daga wurin 'yan bindigar.

KARANTA: Alhaji Ahmed, tsohon dan takarar gwamna, jigo a PDP ya rasu

Onyeaku ya ce dakarun rundunar atisayen Sahel Sanity ne suka samu nasarar kashe 'yan bindiga biyar yayin kowanne musayar wuta da 'yan ta'addar a kananan hukumomin Batsari da Faskari.

Katsina: An yi kazamar musayar wuta, 'yan bindiga fiye da 10 da soja daya sun rasu
Katsina: An yi kazamar musayar wuta, 'yan bindiga fiye da 10 da soja daya sun rasu
Asali: Twitter

"Mun samu bayanan sirri da suka bawa dakarun soji nasarar datse tawagar 'yan bindiga a Garin Inu da ke yankin karamar huumar Batsari da Bugaje da ke yankin karamar hukumar Jibiya.

"Sojojin mu sun yi musayar wuta da 'yan bindigar tare da kashe biyar daga cikinsu nan take yayin da wasu da dama suka gudu da raunukan harbin bindiga.

KARANTA: Dalibin jami'a ya kashe iyayensa da sauran mutanen gidansu, ya ce sun cancanta su mutu

"Dakarunn soji sun bi sahun 'yan bindigar inda suka samu nasarar gano bindigu uku kirar Ak47 da carbi 18 na alburusai.

"Kazalika, a ranar 10 ga watan Janairu, 2021, sojojin da ke aiki a Sabon Layi sun ci karo da wasu 'yan bindiga a Unguwar Rimi da ke yankin Maigora a karamar hukumar Faskari, inda suka fafata a wata kazamar musayar wuta.

"Sojojin mu sun samu agaji daga abokan aikinsu daga Faskari wadanda suka tayasu ragargazar 'yan bindigar daga jirginsu mai saukar ungulu, hakan ya tilasta 'yan bindigar tserewa zuwa cikin surkukin daji.

"Sai dai, kafin su kai ga tserewa, dakarun soji sun hallaka biyar daga cikinsu yayin da wasu daga cikinsu suka gudu da raunukan harbin bindiga," a cewarsa.

Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke kashe jama'a a Nigeria

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu dalilai hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin baya kungiyar Boko Haram a cikin wannan shekarar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel