Fasto Yunana: Shekau yana cikin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria

Fasto Yunana: Shekau yana cikin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria

- Babban Fasto a Cocin Anglica da ke jihar Borno, Desmond Yuana, ya ce Shekau yana fama da matsananciyar rashin lafiya

- Fasto Yuana ya ce nan bada dadewa ba Shekau zai fito ya nemi afuwar jama'a sakamakon mawuycin hali da yake ciki

Desmond Yuana, babban fasto a Cocin Angalika da ke Jihar Borno, ya ce shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yana fama da matsananciyar rashin lafiya kuma yana bukatar addu'a daga wurin 'yan Nigeria.

Da ya ke magana yayin wa'azin da ya gabatar ranar Lahadi, Yuana ya ce an yi masa wahayi a daren ranar Asabar cewa Shekau yana fama da matsananciyar rashin lafiya, kamar yadda TheCable ta rawaito.

A cewarsa, Shekau yana neman addu'a daga wurin Kiristoci da Musulman da ke zaune a Maiduguri tare da bayyana cewa kwanan ma zai fito ya nemi afuwa.

Kalaman Fasto Yuana na zuwa wata daya bayan Mohammed Adam, matshin mayaki a kungiyar Boko Haram, ya tabbatar da cewa Shekau ya nakasa, ba zai kara tafiya daidai kamar sauran lafiyayyun mutane ba.

KARANTA: Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja

Fasto Yunana: Shekau yana cikin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria
Fasto Yunana: Shekau yana cikin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria
Asali: Twitter

Matashin mayakin, wanda dakarun rundunar soji suka kama, ya ce Shekau ya samu raunuka a wani luguden wuta da sojoji suka yi a sansanin 'yan Boko Haram.

KARANTA: Kano: 'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kan titin zuwa gidan Zoo

A cewarsa, lamarin ya faru ne a yankin Tumbuktu da ke cikin dajin Sambisa, babbar maboyar kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

A wani faifan bidiyo da TheCable ta yi ikirarin cewa ta gani, Adam ya bayyana cewa yanzu Shekau ba zai iya jagorantar mayakansa zuwa wata fafatawa ko artabu ba.

An dade ba'a ga Shekau a tsaye ya na magana a faifayen bidiyo da ya fitar a 'yan kwanakin baya bayan nan ba, kamar yadda ya saba yi a baya.

A ranar 5 ga watan Janairu ne Legit.ng ta rawaito cewa a karo na farko cikin sabuwar shekarar 2021, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon faifan sakon.

A cikin sabon sakon faifan sautin muryar, Shekau ya yi gargadi na musamman ga babban malamin addinin Islama, Sheikh Dakta Ahmad Gumi, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta sanar.

Shekau ya gargadi Gumi akan alakanta kungiyar Boko Haram da Fulanin da ke yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: