Shekau ya saki faifan sako na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi

Shekau ya saki faifan sako na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi

- Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki bidiyonsa na farko a cikin sabuwar shekarar 2021

- A cikin sabon faifan , Shekau ya gargadi babban addinin Islama da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi

A karo na farko cikin sabuwar shekarar 2021, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon faifan sakon sautin murya tare da yin gargadi na musamman ga babban malamin addinin Islama, Sheikh Dakta Ahmad Gumi.

Jaridar Daily Nigerian ce ta sanar da hakan a wani takaitaccen sako da ta wallafa a shafinta a dandalin tuwita.

Shekau ya gargadi Gumi akan alakanta kungiyar Boko Haram da Fulanin da ke yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

A ranar Lahadi ne Sheikh Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ziyarci wasu rugagen Fulani da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa rugagen da Babban Malamin ya ziyarta sun kasance tamkar tarko wurin matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Amma, a faifan sautin murya mai tsawon mintuna 16 da ya saki ranar Talata, Shekau ya jaddada cewa kungiyarsa ba ta amfani da wasu 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja ko jihar Neja.

KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari

"Ba ma amfani da kowa wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

"Mun san akwai masu amfani da sunan kungiyar mu wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, amma bama tare da duk irin wadannan kungiyoyi.

Shekau ya saki faifan bidiyo na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi
Shekau ya saki faifan bidiyo na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi @Premiumtimesng
Asali: Twitter

"Zamu yi aiki da duk mai son yin aiki tare da mu ko a Kaduna, Lagos, Benin, ko Amurka, amma mu kira muke yi zuwa ga Allah, ba dimokradiyya ko sabawa addini ba.

KARANTA: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna na wulakanci

Yayin da ake tattaunawa da shi, Sheikh Gumi ya bayyana damuwarsa a kan yadda hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama abar tsoro saboda rashin tsaro tare da sanar da cewa jahilci ne yasa ake amfani da Fulani wajen aikata garkuwa da mutane.

A cewarsa, bawa irin wadannan Fulani ilimin addini ko na zamani shine kadai mafita daga kangin jahilcin da ya jefasu cikin irin mummunar rayuwa.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa wani mayakin kungiyar Boko Haram da aka kama ya bayyana cewa Shekau ya samu nakasa a kafafunsa, a saboda haka ba ya iya tafiya daidai.

Matashin mayakin mai suna Mohammed Adam, wanda dakarun rundunar soji suka kama, ya ce Shekau ya samu raunuka a wani luguden wuta da sojoji suka yi a sansanin 'yan Boko Haram.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a yankin Tumbuktu da ke cikin dajin Sambisa, babbar maboyar kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng